Dalilin da ya sa ECOWAS ta janye takunkumin Nijar da Mali da Burkinafaso 

Dalilin da ya sa ECOWAS ta janye takunkumin Nijar da Mali da Burkinafaso 

Ƙungiyar Raya Tattalin Arzkin Ƙasashen Afirka ta Yamma, Ecowas ta ɗage tarin takunkuman da ta ƙaƙaba wa ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso da kuma Giunea.

Ƙungiyar ta ɗauki matakin ne a wani taron shugabannin ƙasashen ƙungiyar da aka gudanar a Abuja babban birnin Najeriya.

Ƙungiyar ta ce a yanzu za ta iya gayyatar ƙasashen huɗu zuwa tarukanta da suka shafi tsaro da zaman lafiya.

Ecowas ta ce ɗage takunkuman - wanda zai fara aiki nan take - ta yi shi ne bisa dalilai na jin kai.

Takunkuman sun haɗa da na zirga-zirga tsakanin ƙasashen, da na kasuwanci da tattalin arziki.

Huka kuma ƙungiyar ta jaddada kiranta na sakin hamɓararreb shugaban Nijar Mohamed Bazaoum da sojojin ƙasar ke ci gaba da yi wa ɗaurin talala.

Ecowas ta kaƙaba wa ƙasashe takunkuman ne bayan da sojoji suka kifar da gwamnatocin fara hula a ƙasashen.

Daga cikin takunkuman da ƙungiyar ta ƙaƙaba wa ƙasashen sun haɗa da rufe iyakokin ƙasashen da na ƙungiyar da kuma yanke wutar lantarki a Nijar da sauran takunkuman karya tattalin arziki.

A makonnin baya-bayan ne ƙasashen Nijar, MAli da Burkina Faso suka ayyana ficewa daga ƙungiyar bayan da suka zargi ƙungiyar Ecowas da ƙaƙaba musu takunkuman karya tattalin arziki.

Ecowas ta riƙa fuskantar matsin lamba daga ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane kan ta ɗage wa ƙasashen takunkuman.

Ko a makon da ya gabata ma tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya Janar Yakubu Gowan wanda shi ne mutum ɗaya tilo da ya rage cikin shugabanin da suka kafa ƙungiyar, ya yi kira ga shugabanninta da su ɗage wa ƙasashen takunkuman.

Nijar ta samu kanta cikin takunkuman Ecowas bayan da sojojin kasar suka kifar da gwamnatin farar hula da Mohamed Bazoum cikin watan Yulin shekarar da ta gabata.