Home Daga Marubutanmu Dalilin da ya sa babu wani gwamna da ba zai yi Tinubu...

Dalilin da ya sa babu wani gwamna da ba zai yi Tinubu a 2027 ba – Uba Sani 

1
0

Dalilin da ya sa babu wani gwamna da ba zai yi Tinubu a 2027 ba – Uba Sani 

Uba Sani, gwamnan jihar Kaduna, ya ce abu ne mai wuya a samu wani gwamna a Najeriya da zai kalubalanci sake tsayawar Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.

Uba Sani ya bayyana hakan ne a wajen bude taron tattaunawa na kwana biyu tsakanin gwamnati da al’umma, wanda Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello (SABMF) ta shirya a Arewa House, Kaduna.

Ya ce: “Baya ga haka, babu wani shugaban kasa a tarihin Najeriya da ya ba gwamnonin jihohi da gwamnatocin jihohi goyon baya kamar yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke yi a yanzu.”

“Sakamakon haka, da wuya a samu wani gwamna a Najeriya da zai tsaya ya kalubalanci shugaban kasa.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here