Dalibbai da Bankin Musulunci Sun Kubutar da Mutum 6 a Gidan Yari da Bayar da Tallafi a Sakkwato

Dalibbai da Bankin Musulunci Sun Kubutar da Mutum 6 a Gidan Yari da Bayar da Tallafi a Sakkwato
 

Kungiyar dalibbai da Bankin musulunci ya tallafa  tare da kubutar da  fursunoni guda shidda a babban gidan yarin Sokoto.

 
Sakataren kungiyar Dakta  Abubakar Sadiq Muhammad na kasa ya bayyana cewa makasudin wannan tallafin domin ganin fusunonin sun yi sallah cikin farinciki.
 
Dakta Abubakar Sadiq Ya kara dacewa wadanda aka kubutar   su ne wadanda kananan kudi yasa suke tsare a gidan yarin ba tare da samun masu biya musu ba.
 
Ya yi kira ga masu hannun da shuni da su taimakawa wadanda ke zama a gidan yarin mussaman lokacin bukukuwan sallah domin suma su kasance cikin farinciki.
Wannan kungiyar ta dalibban taimako da jinkan al'umma ne ta sanya a gaba domin ganin sun ba da tasu gudunmuwa a haujin cigaban jama'a da sanya su cikin farinciki.
Kungiyar ta shahara a wurin taimako da bayar da agaji ga wadanda ke bukatar taimako a jihar Sakkwato.
 
Kayan  tallafin da aka raba  sun hada da buhun gari, takalma, sabulun wanka da na wanki, ruwan sha da dai sauransu.