Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya sanya dokar ta baci ta awa 24 a jihar Sakkwato domin dawo da zaman lafiya a birni da kewayen jihar.
Dokar za ta fara aiki nan take ba bata lokaci kowa zai takaita zirga-zirga.
A safiyar yau ne aka tashi da zanga-zangar lumana domin kira a saki mutanen da aka kama da zargin sun kashe Daborah Yakubu kan ta zagi manzon Allah.
Zanga-zangar lumana ta juya zuwa tashin hankali a wasu unguwanni abin da ya kai ga sanya dokar nan take.





