Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya ce zai fara tuntuba kan tsayawa takarar shugaban kasa da mutane da dama ke bukatar ya fito a zaben 2023 dake tafe zai bayyana matsayarsa a karshen watan Fabarairu.
Gwamna Tambuwal a harabar hidikwatar jam'iyar PDP bayan ya kaddamar da babban ofishin jam'iya na jiha a jiya Litinin ya ce kowane al'amari na Allah ne yana yin yanda yake so haka abubuwa ke tasowa don sun gode Allah haka siyasa take a cikin gwagwarmaya ake yinta.
"Wannan jiha Allah ya albarka ce mu da jagorori ina tunawa a 2011 'yan majalisa suka bukaci na tsaya takarar jagoran majalisar wakillai na gaya masu cewa mu a jiharmu ta Sakkwato muna da biyayya da shugabaninmu, ba zan karbi kiran ba sai sun zo Sakkwato sun nemi tsohon shugaban kasa Shehu Shagari in ya ce na yi zan yi, Sai kun nemi gwamnan Sakkwato na lokacin Mai girma Sarkin Yamma Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko in ya ce in yi, ku dawo na amince ba gudu ba ja da baya," a cewar Tambuwal.
Ya yi karin haske kan haka ya ce dalilin wannan duk abin da za ka yi ka fara shi daga gida domin samun albarka da amincewarsu ba a iya yi maka yankan baya haka aka yi lamarin.
Tambuwal ya ce sun yi shawarar fara tuntuba daga gida don sanin matsayar PDP a Sakkwato na neman da ake yi na fara tuntuba kan shugabanci a Nijeriya "na ji bayyanai ga dattawa da matasa da mata na ji bayani ga shugaban jam'iya kan haka na aminta da na fara tuntuba kan neman takarar shugabancin Nijeriya.
"Na fara wannan aikin ne daga yau(litinin) za mu kare wannan aikin na tuntuba na dawowa 'yan Nijeriya da bayanin karshe abin aka cimma a karshen watan biyu da ikon Allah," a cewarsa