Gwamnatin jihar Plateau ta rufe makarantu saboda barkewar cutar mashako
Gwamnatin Jihar Plateau ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun firamare da sakandare na jihar na wani dan lokaci, domin dakile yaduwar cutar mashako wato diphtheria.
Gwamna Caleb Mutfwang ne ya bayar da umarnin, wanda zai fara aiki daga Litinin, 7 ga Satumba, 2026, kuma zai ci gaba har sai an ba da wani sabon umarni.
Rahotanni sun ce mutane 23 sun mutu sakamakon cutar a jihar, yayin da aka samu mutane 148 da ake zargin sun kamu da ita. A halin yanzu, marasa lafiya takwas na jinya a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH), yayin da wasu biyar ke kwance a Plateau Specialist Hospital.
Kwamishinan lafiya na jihar, Nicholas Baamlong, ya ce gwamnati ta sanar da NCDC tare da karbar kayan aikin da ake bukata domin tattara samfura da aika su dakin gwaje-gwaje.
Ya bukaci iyaye su tabbatar da cewa ‘ya’yansu sun kammala allurar rigakafin diphtheria, tare da neman agajin likita cikin gaggawa idan yara suka fara nuna alamun cutar.
Gwamnatin ta kuma kara kaimi wajen wayar da kan jama’a da gudanar da allurar rigakafi a yankunan da cutar ta fi kamari, tare da kira ga jama’a da su kiyaye tsafta da guje wa cunkoso.






