Cutar Koda na kara yaduwa a Najeriya – Likitoci

Cutar Koda na kara yaduwa a Najeriya – Likitoci

Kwararrun likitoci kan cututtukan dake kama Koda sun yi kira ga gwamnati ta tsara hanyoyin da za su taimaka wajen rage tsadar maganin cututtukan a kasar nan.

Shugaban kungiyar likitocin Koda na Najeriya Adanze Asinnobi ce ta yi wannan kira a taron likitoci da kwararrun masana kimiyya da ake yi duk shekara wanda aka yi ranar Laraba a Kano.

Adanze ta yi wannan kira ganin yadda cutar ke ci gaba da yaduwa sannan da yadda masu fama da cutar ba su iya samun magani saboda tsadar da yake da shi a asibitoci.

Taken taron bana shine “Hanyoyin rage yaduwar cutar da yadda za a samu sauki wajen samun maganin cutar”. An zabi wannan take domin samun hanyoyin dakile yaduwar cutar da rage tsadar farashin maganin a kasar nan.

Adanze ta yi kira ga gwamnati da masu ruwa da tsaki su hada hannu domin Samar da ingantattun kayan aiki na zamani domin kula da masu fama da cutar a asibitocin kasar nan.

Ta Kuma yi kira ga gwamnati da ta Saka cutar a cikin tsarin inshorar lafiya domin talakawan da suka kamu da cutar su iya samun kulan da ya kamata.

Idan ba a manta ba sakamakon binciken da kungiyar likiyocin Koda ta Najeriya suka gudanar ya nuna cewa akalla mutum miliyan 25 dake dauke da cutar Koda a kasar nan.

Hakan na da nasaba da matsalolin rashin sani, rashin isassun asibitocin samun kula, tsadar farashin kula da rashin kwararrun ma’aikatan da za su rika kula da mutanen da suka kamu da cutar.

Hanyoyin kamuwa da cutar Koda.

1. Yawan amfani da man dake canja kalan fatar mutum.

2. Yawan Shan magunguna musamman wadanda ake Sha ba tare da izinin likita ba.

3. Rashin shan ruwa a lokacin da ya kamata.

4. Shan giya da busa taba sigari.

5. Kamuwa da cutar Kanjamau, Hepatitis, ciwon siga wato ‘Diabetes’.

6. Jin rauni a Koda.

7. Kiba da rashin motsa jiki.

8. Shakan gurbatacen iska.

9. Yawan Shan kayan Zaki da gishiri.