CUPS CAKE

       CUPS CAKE

BASAKKWACE'Z KITCHEN


          

      

ABUBUWAN BUƘATA
•Flour rabin loka/mudu
•Butter simas 2
•Kwai 15
•Sugar gwangwani 2
•Baking powder cokali daya table spoon
•Flavor quater tea spoon.


YANDA ZAKI HAƊA
Ki sami kwano ko roba ki zuba Butter ɗinnan duka sai ki zuba Sugar, ki juya su ki yi ta buga shi domin Sugar ɗin ya narke.
Daga nan sai ki zuba ƙwai ki yi ta buga shi sosai, idan kina da Mixer ma zai fi haɗuwa sosai.
Sai ki zuba flour da baking powder da flavor ki yi ta bugawa, har sai kin ga ya haɗe. Wasu kuma suna zuba flavor da baking powder a flour kafin su juye.
Sai ki sami murfi ki rufe, ki je ki kunna oven, idan gwangwanin cake kike dashi sai ki shafa Butter ko Mai, idan kuma cup cake kike dashi to sai ki zuba kwaɓin ki sa a Oven ki gasa.


Note: Flavor na gari zaki yi amfani dashi, sannan idan kika cika domin kiyi gwaninta toh zayyi caccaki a saman cake din.
Sannan Baking Powder din na gwangwani zaki yi amfani dashi, ba na roba ba, domin shine zai sa ya tashi sosai.
Wannan shine the most simplest way na yin cake. Ki gwada ɗan kaɗan zaki ga canji. Ko baki sa milk ba zayyi daɗi.
Idan zaki yi ɗan kaɗan kuma ga yawan da zaki sa abubuwa saboda kada ki yi dayawa yazo bayyi kyau ba ki yi asaran kaya


```NA GWANGWANI UKU```
INGREDIENTS:
Flour 3 gwangwani
6 eggs manya
1/2 tea spoon of baking powder
Flavor 1 tea spoon ko 1/2
Butter simas 1
Sugar 1 gwangwani

YANDA ZAKI HAƊA
Ki sami mixing bowl ki zuba sugar, sai ki zuba butter ɗinki, ki sa su haɗu sosai, har sai Kin ji Sugar ɗin ya narke sosai.
Ki sami ƙwan ki buga a wani kwano, sai ki juye ciki, ki cigaba da juyawa, idan suka haɗe sai ki zuba ma flour ɗinki baking power ki tankaɗe, sai ki na zubawa kina juyawa har ya shige duka, idan ya hadɗ sosai sai ki zuba flavor ɗinki, ki cigaba da juyawa.
Daga nan sai ki ɗauko gwangwanin cake ɗinki ko toaster ki sa butter ki fara Gasawa. ƙamshi zaki ji ya cika ko Ina kuma zayyi daɗi. Simple and easiest way kenan na yin cake.

08167151176
MRSBASAKKWACE