Cikaken jawabin Gwamna Tambuwal na ranar 'yan cin kan Nijeriya shekara 61

Matsalolin rashin tsaro sun ta'azzara a Ƙasar mu, a halin yanzu babu wani yankin Kasar nan da ba ya fuskantar wani nau'in matsalar rashin tsaro, wannan ne yanayin da munka tsinci kammu a yau na kisan kiyashi da ake yi wa al'umma tare da kassara tattalin arzikin jama'a. Waɗannan rikice-rikicen sauya albarkokin yawan ƙabilun mu ya zuwa tafarkin farraƙa, ko a tarihi, Najeriya ba ta taɓa shiga yanayin rabuwar kai ba irin wanda ta ke fuskanta a halin yanzu ba. 

Cikaken jawabin Gwamna Tambuwal na ranar 'yan cin kan Nijeriya shekara 61

 

Assalamu alaikum wa rahmatullah

 

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda Ya raya mu ya zuwa wannan rana ta sake zagayowar bukin' yancin Ƙasar mu Najeriya karo na 61

 

2. Tare da alhini mu ke tuna alƙawurra da kyakkyawar fatan da an ka kafa Ƙasar nan ta mu, bisa ga amannar samun makoma mai kyau. Mutum ba ya bukatar wani zurfin tunani kafin ya fahimci dalilan da suka sanya Kakannin mu da suka kafa wannan Ƙasar sun ka ɗora mu a kan wannan tafarki. 

 

 3. Haƙiƙa, mu mutane ne da Allah Ya wa albarka kuma Ya tada mu a ƙasa mai albarka da har ake ganin mun mallaki dukkan arzuƙƙa da halayyar da za mu iya tinƙaho da su a gaban sauran Ƙasashen duniya 
 
4. Sai dai kash! Matsalolin da mun ka ƙirƙira da hannayen mu sun ci gaba da zamowa tarnaki ga samun ci gaban da ake yi wa Najeriya fatan samu. Har yanzu muna kokawa da kokarin samun tsarin dimokaraɗiyya managarci. Matsalolin rashin kyawawan tsare-tsare da rashin bin doka da oda sun jefa tattalin arzikin Ƙasar mu cikin ruɗani tun ma kafin zuwan annobar cutar Korona(Covid-19) 
 
5. Matsalolin rashin tsaro sun ta'azzara a Ƙasar mu, a halin yanzu babu wani yankin Kasar nan da ba ya fuskantar wani nau'in matsalar rashin tsaro, wannan ne yanayin da munka tsinci kammu a yau na kisan kiyashi da ake yi wa al'umma tare da kassara tattalin arzikin jama'a. Waɗannan rikice-rikicen sauya albarkokin yawan ƙabilun mu ya zuwa tafarkin farraƙa, ko a tarihi, Najeriya ba ta taɓa shiga yanayin rabuwar kai ba irin wanda ta ke fuskanta a halin yanzu ba. 
 
6. Tabbas dai a nan shi ne, kyakkawan fata da manufofin da Kakannin mu sun ka kafa Ƙasar nan suna nan raye a zukatan mu duk kuwa da ɗimbin kalu-balen da mu ke fuskanta. Haɗin kai kawai mu ke buƙata domin cimma kyawawan manufofin mu, a matsayin mu na al'umma ɗaya tabbas za mu iya kunyata maƙiyanmu, mu kuma tozarta munmunar manufar su akan mu, mu tashi tsaye haiƙan domin kai Ƙasar mu gaci. 
 
7. Ya zamanto wajibi mu yi aiki tare domin ceto kan mu daga guguwar Ƙabilanci da Ɓangarance da kuma sauran halayen rashin kishin ƙasa. Alhamdulillah, akwai kyakkawan fata da muke da shi a sakamakon azama da ƙwazonda 'Yan Najeriya suke da shi wanda ya san ya ake ganin cancantar su ana basu matsayin jagorancin muhimman ƙungiyoyi da hukumomin duniya. 
 
8. A nan ina kira ga' Yan Najeriya da mu yi amfani da wannan lokaci domin mu sake tunani da nufin cimma matsayar gudummawar da za mu bayar domin cimma wannan buri. Ya zamo wajibi mu yanke wa kammu hukumci kan irin alummar da mu ke son zamowa da nau'in shugabanci da mu ke buƙata domin fitar da Ƙasar mu daga halin da take ciki. 
 
9. Baya kamata mu ƙara ta'azzara halin da Ƙasar mu take ciki a halin yanzu don cika muradunmu na son-rai a matsayi mu na ƙungiyoyi ko ɗaiɗaikun mutane. Yan Najeriya basu da wajabcin bin duk wani ra'ayi da saɓawa abin da ya dace. 
 
10. Haƙaƙanin muradin 'Yan Najeriya a yau shi ne samar da ingantaccen yanayi da zai tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin su, domin cimma ɗaiɗaikun muradunsu da na ƙasa baki ɗaya a cikin adalci da kwatanta gaskiya a tsakanin dukkan ' Yan Ƙasa. 
 
11. A nan ina ganin ya dace in janyo hankalin mu ga babban batu a yau, wato lamarin tsaro. A yayin da gwamnatoci ke ƙoƙarin ɗaukar matakan hana kisan kiyashin da ake wa al'umma. Ina son in yi kashedi da kakkausar murya ga ma su son sanya siyasa ko ɓangaranci a cikin wannan matsala da su daina, domin ita matsalar tsaro matsala ce da ke iya shafuwar kowa ba tare da la'akari da banbamcin Yare ko na addini ko kuma ɓangare ba. 
 
12. A maimakon haka ya kamata mu san da cewa wajibi ne mu tashi tsaye baki-ɗayan mu ɗauki matakan bayar da gudummawa a magance wannan matsala a duk faɗin Kasar nan. Saboda babu wata al'umma da ke iya samun ci gaba a cikin halin rashin tsaro. 
 
13. Anan jahar Sokoto ba za mu yi watsi da bukatoci da muradun jama'ar mu ba a kowane fannin rayuwa. Mun duƙufa a wajen samar masu romon dimokaraɗiyya na fili da na ɓoye. 
 
14. A yayin da mun ka buɗe kofofin gwamnatin mu ga kowa da kowa. Tun da mun ka karɓi jagorancin wannan jaha a shekara ta 2015 mun samarda cigaba mai mai yawa da ma'ana a ɓangarorin Ilimi da kiyon lafiya da bunƙasa noma da samarda ababen more rayuwa a yankunan karkara da samar da ci gaban jama'a. 
 
15. Mu na murnar zagayowar ranar samun 'Yancin Ƙasar mu wannan yanayi na rashin tsaro wanda a sanadin sa mun rasa rayukkan jama'a da dama. A madadin gwamnati da kuma jama'ar jahar Sokoto ina miƙa saƙon ta'aziyya ga iyalai da yan uwan waɗanda sun ka riga mu gidan gaskiya, Allah Ya gafarta ma su, kuma Ya ba mu hanƙurin jure rashin, Ya kuma kawo sauƙi ga waɗanda suka ji rauni masu jinya a gida da asibitoci. 
 
16. A yayin da muke juyayin abin da yake faruwa a wasu sassan jahar nan da wannan ibtila'in ya shafa, ina jinjinawa jam'i an tsaron mu da sarakuna da sauran masu hannu ga lamarin tsaro, a yayin da muke aiki tare domin magance wannan ƙalubalen ina mai jaddada ƙudurin gwamnatin Jaha na yaƙi da ayukkan yan bindiga da sauran miyagun ayukka ta hanyar samarda dukkanin tallafi da gudummawa da ake bukata ga jama'a da jam'i an tsaron mu. 
 
Na gode , wassalamu alaikum.