Cece-Ku-Ce Kan Rashin Halartar Tambuwal Da Lamido a Wurin Yaye Jami’an Tsaron Sakkwato
Rashin halartar Sanatoci biyu Sanata Aminu Waziri Tambuwal da Sanata Ibrahim Lamido dake wakiltar Sakkwato a majalisar tarayyar Nijeriya ya haifar da cece ku ce a jiha ganin yanda suke da matukar muhimmanci ga halartar taron.
Gwamnatin jihar Sakkwato karkashin jagorancin Dakta Ahmad Aliyu Sokoto ta kaddamar da jami’an tsaron jiha sama da mutum 2000 domin cigaba da aikin tsare yankunan da ke fama da 'yan bindiga a fadin jiha.
Bukin yaye jami'an tsaron da aka yi ranar Assabar ya samu halartar Gwamononi bakwai, Bauchi, Benue, Filato, Kano, Katsina, Kebbi da kuma Zamfara.
Mataimakin Gwamnan Jigawa da tsoffin Gwamnonin Sakkwato uku Malam Yahaya Abdulkarim da Alhaji Attahiru Bafarawa da Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko sun samu halarta.
Rashin halartar Sanatoci biyu Sanata Aminu Waziri Tambuwal da Sanata Ibrahim Lamido dake wakiltar Sakkwato a majalisar tarayyar Nijeriya ya haifar da cece ku ce a jiha ganin yanda suke da matukar muhimmanci ga halartar taron.
Aminu Isah mazauni a Sakkwato ya ce a gaskiya na yi matukar mamakin rashin halartar Sanata Lamido a wurin taron nan domin in da yake wakilci waton Sakkwato ta Gabas sun fi kowa fadawa cikin matsalar tsaron nan, duk da yana kokarinsa amma yakamata mu ganshi a taron.
Ya ce duk da akwai zargi da ake yadawa a gari baya tare da gwamnatin Sakkwato a yanzu, amma yakamata ya jingine wannan in har akwai, domin harkar siyasa daban-harkar tsaro daban. In kuma ba a gayyace shi ba tau wannan ma yana da gaskiyarsa a rashin zuwan.
Muhamma Kabiru daga karamar hukumar Rabah ya ce Lalle bai dace Sanata Ibrahim Lamido ya ki zuwa wurin taron ba don mu hadin kansu muke so gaba daya a yi tafiya tare a magance mana matsalar tsaro, ina kira ga shugabanni su hada kai don kawar mana da matsalar tsaro a yankinmu da jiha.
Bello Kabiru ya ce rashin ganin Sanata Tambuwal ne yafi ban mamaki domin shi tsohon gwamna ne, kuma a harkar siyasarsa baya da riko a sanda yake mulki bai dauki dan adawa abokin gaba ba, akwai bukatar 'yan jarida su binciki lamarin nan, an gayyyace shi kuwa?
Ya ce ni a wurina a kan rashin halartarsa ban san mai laifi ba domin zai yiwu ba a gayyace shi ba, in ko an gayyace shi bai zo ba tau bai kyauta ba, kuma ya sauya daga yanda aka san shi a harkokin siyasarsa.
managarciya