Burkina Faso da Mali sun ƙaurace wa taron hafsoshin soji na Afirka da ke gudana a Najeriya
Kasashen Burkina Faso da Mali sun kaurace wa babban taron shugabannin sojojin Afirka da Najeriya ta shirya a Abuja, lamarin da ya nuna rashin jituwar diflomasiyya tsakanin kasashen Sahel masu mulkin soja da makwabtansu.
Sai dai Nijar ce kadai daga cikin kasashen Alliance of Sahel States (AES) da ta halarci taron, inda jakadarta mai kula da harkokin tsaro, Colonel Major Soumana Kalkoye, ya wakilta ta.
Babban Hafsan Sojin Najeriya, Christopher Musa, ya bukaci sabon tsarin hadin gwiwa na tsaro karkashin jagorancin Afirka, yana mai cewa kalubalen tsaro “ba su da iyaka” kuma dole a fuskance su tare.
Najeriya da Nijar sun taba samun sabani bayan juyin mulkin 2023, amma daga baya suka rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro.
Sai dai janyewar Nijar daga rundunar hadin gwiwa ta yankin ya kawo cikas ga yaki da ’yan ta’adda a yankin Tafkin Chadi.
managarciya