Bunƙasa ilmin Islama: Makaranta ta yaye Dalibbai 197 a Zamfara

Bunƙasa ilmin Islama: Makaranta ta yaye Dalibbai 197 a Zamfara

Makarantar Mu'assasatu Shehu Malam Babba Li ta'alimi dake Kaura Namoda ta gudanar da bikin yaye Ɗalibbai 197*

Daga Yahaya Mahi Na Malam Babba 

A ranar Lahadi 17 ga watan Agusta, Makarantar Mu'assasatu Shehu Malam Babba li ta'alimi a Unguwar shiyar Muhammadu dake karamar hukumar mulkin Kaura Namoda jahar Zamfara ta gudanarda bikin yaye Ɗalibbai 197 na rukunin karatuka 3 da makarantar ke gabatarwa.


Rukuni na farko shine bangaren islamiyya da aka yaye Ɗalibbai 117 wanda wannan shine karo na 14, yayinda bangaren kulliya na karamar Sakandare aka yaye Ɗalibbai 45 wanda shine karo na 4, yayinda a bangaren Babbar Sakandare aka yaye Ɗalibbai 35 kuma shine karo na farko bayan cikar shekaru 3 da kafuwar wannan sashe.

Tun da farko an gayyato Sheikh Malam Nasiru liman kaura, babban limamin Masallacin juma'a na farko ya buɗe taro da Addu'a

Bayan buɗe taro da Addu'a aka gayyato dalibi Ahmad Bashir Faruku ya karanto wasu daga cikin ayoyin Alkur'ani Mai irma daga nan aka gayyato Shugaban sashen kulliya Mal Tihami Ibrahim Dasuki ya gabatar da jawabin Maraba da mahalarta da kuma tarihin kafuwar wannan makaranta

Malam Tihami ya bayyana cewar an kafa wannan makaranta ya kafu ne tun Zamanin Rayuwar Malam Muhammadu Babba a tsarin karatun allo kafin daga bisani ya dawo na zamani ashekara 1971 daga bisani a shekara ta 2010 aka yimata rijista da hukumar ilmi ta jaha.

Ya ci gaba da cewar ta fara karatu da dalibai 80 da malamai 6 amma kawo yanzu a sashen islamiyya akwai Ɗalibbai 1530 da malamai 40, ashekara ta 2019. Wannan makaranta ya bude sashen kulliya da dalibai 40 malamai 17 amma kawo yanzu akwai Ɗalibbai sama da 400 da malamai 39.

Shima a nasa jawabi Shugaban Uwaye da Malamai kuma Khalifan Zawuyyar Shehu Malam Babba wato Khalifa Malam Abubakar Atiku Maisuna Na Malam Babba ya bayyana jin dadinsa ga yanda Tsarin wannan makaranta ke tafiya kuma ya yaba ga jajircewar malaman saboda inda babu jajircewarsu baza'a cimma wannan nasara ba.

Wasu daga cikin sashen Ɗalibban islamiyya sun gabatarwa Almunaƙisha ilmiyya mai taken *baiwa 'ya'ya mata ingantacciyar tarbiyya ya fi muhimmanci akan baiwa maza* , yayinda kowane bangaren ya baiwa nasa bangaren kariya aƙarshe dai mata suka cinye wannan gasar, Suma bangaren kulliya sun gabatar da wata kwarya kwaryar Tamsiliyya ta 'yan Daƙiƙu tsakanin kuɗi da ilmi yayinda kowane sashe ya fafata da juna

Shima Shugaban Ƙaramar hukumar mulkin Kaura Namoda Com Mannir Mu'azu Haidara ta bakin Kamsila mai wakiltar Mazabar Sarkin Mafara Sarkin baura da ya wakilceshi ya nuna godiya ga iyaye da malaman makarantan akan jajircewarsu tun daga kafuwar wannan makaranta har zuwa yau.

Ya bayarda gudummawar kuɗi N100,000 Amadadin shugaban karamar hukumar haka kuma shi ƙashin kansa ya bayarda N20,000 ga hukumar makaranta, N20,000 ga Ɗalibbai da sukayi kasance kasance awurin, N20,000 ga kwamitin gudanarda bikin. Shima Kamsila mai wakiltar Sakajiki ya bada N10,000


 Karshe aka gayyato Mai martaba Sarkin kiyawan kaura Namoda Major Dr Sanusi Muhammad Ahmad Asha Khadimul Kur'an ya gabatar da jawabn karfafa guiwa da muhimmancin ilmin inda yayi kira ga iyaye da su dage ga tarbiyyar 'ya'yansu, ya nuna cewar dukkanin tashe tashen hankulla da taadanci suna faruwa ne idan babu ilimi da tarbiyya, daga bisani ya gabatarda gudummawar N30,000 ga hukumar makaranta kuma ya damƙa kyaututtuka ga dalibai da sukayi hazaƙa da kuma bayarda Takardar sheda ga kowane dalibi ɗaya bayan ɗaya.

Wasu daga cikin dalibai da na zanta dasu A'isha Habib, Hussaina Haruna, Zikirullahi Abubakar, Nazifi Idris, Khadijah Sayyid duk sun nuna godiya ga Allah da ya nuna masu kammala wannan karatun.

Bikin ya samu halartar Mataimakin Shugaban makarantar Fasaha da ƙere ƙere ta gwamnatin tarayya dake Kaura Namoda Dr Yusuf Nasir, Babban limamin masallacin juma'a na biyu liman Malam Badamasi, Shugaban Majalisar Shura ta Darikar Tijjaniyya Liman Malam Junaidu Usman, Malam Idris Aliyu, Malam Salman, Malam Sani Dan tudu, Malam Sulaiman Baban Fadima, Hakimin  Unguwa Bello Muhammad, Manyan Iyaye, 'yan kasuwa, Malaman makarantun islamiyyu, hakimmai, kungiyoyin Addinai da sauran al'ummar yankin