Buhari Ya Gana da Gwamnan CBN, Tambuwal, Bagudu Kan Karancin Naira 

Buhari Ya Gana da Gwamnan CBN, Tambuwal, Bagudu Kan Karancin Naira 

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya sa labule da shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya, Aminu Tambuwal da shugaban gwamnonin APC, Atiku Bagudu. 

Shugaban ƙasan ya zauna da manyan gwamnonin ne kan halin da ake ciki na karancin sabbin takardun naira guda uku da CBN ya canja.
Duk da har yanzu ba a fitar da bayani sosai ba, amma an fara yada jita-jitar za a kara lokacin karbar tsoffin kudi ne har zuwa watan shidda.
Sai dai 'yan kasa suna koka karancin yawan kudi masu zagayawa ne matsala ba karin wa'adin daina karbar tsoffin kudi ba.