Home Uncategorized Buhari ya ba ministan ilimi umarnin kawo ƙarshen yajin aikin ASUU cikin...

Buhari ya ba ministan ilimi umarnin kawo ƙarshen yajin aikin ASUU cikin mako biyu

2
0

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umarni ga ministan ilimi na ƙasar Malam Adamu Adamu da ya kawo ƙarshen yajin aikin malaman jami’o’in ƙasar.

Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa shugaban ya bayyana haka ne a ranar Talata inda ya bayar da umarni ga ministan ilimin ƙasar da ya sasanta abubuwan da ake taƙaddama a kai cikin mako biyu sa’annan a kai masa rahoto.

A yau Talata Shugaba Buharin ya tattauna da ma’aikatu da masu ruwa da tsaki waɗanda ke da alaƙa da ɓangaren ilimi a ƙasar da za su iya warware wannan tirka-tirkar.

Shugaban ya kira su ne domin ya samu ƙarin bayani kan dalilin da ya sa wannan yajin aikin ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here