Buhari Na Fuskantar Matsin Lamba Gabanin Karewar Wa'adin Mulkin Sa 

Buhari Na Fuskantar Matsin Lamba Gabanin Karewar Wa'adin Mulkin Sa 
 

Daga Abbakar Aleeyu Anache.

 

Watannin 6 gabanin gudanar da babban zabe a Najeriya, matsalolin tsaro na cigaba da dabaibaye mulkin shugaba Muhammad Buhari musamman a yankin arewacin kasar, kama daga yan bindiga da kuma boko haram wadanda a baya-bayan nan suka samu zarra kai farmaki Abuja fadar gwamnatin kasar.

 

Kamfanin dillancin labaran Faransa da ya tattara alkaluma game da irin hare-haren da yan bindiga ke kai wa a sassan Najeriya ya bayyana yadda kasar ta koma abar tsoro fiye da halin da aka shiga kafin zaben 2015: 
 
Idayat Hassan shugaban cibiyar tabbatar da Demokradiyya da cigaban al'umma a Najeriya ya ce akwai bukatar tabbatar da tsaro da lafiyar al'umma a halin da kasar ke ciki musamman la'akari da yadda kowa ya ke cike da fargaba, 
 
Ko a watan jiya kungiyar ISWAP ta kaddamar da farmaki kan gidan yarin kuje mai tazarar kilomita 20 daga filin jirgin saman Abuja tare da sakin daruruwan fursinoni ciki harda kwamandojin Boko Haram 64, yayin da ake fargabar sake fuskantar makamantan hare-haren a wasu gidajen yarin kasar da ya tilsta tsauraran tsaro, 
 
Harin na gidan yarin kuje ya sake bayyana gazawar gwamnatin wajen tabbatar da tsaron al'ummar kasar wanda ke matsayin karon farko da yan ta'adda suka iya aika-aikar a cikin babbar birnin da ke tsakiyar kasar tun bayan hare-haren 2015, 
 
Duk da a watan na jiya yan bindiga sun farmaki wasu shingayen binciken jami'an tsaro yayin da kuma suka farmaki tawagar motocin shugaban kasa, 
 
Cikin wata yunin da ya gabata yan bindiga sun kashe mutane akalla 40 a majami'ar Owo mako guda bayan kisan wasu matafiya mutum 5 a jihar Kogi, 
 
Har zuwa yanzu dai akwai daruruwan dalibai da ke hannun yan bindiga a jihohin Kebbi da katsina da kuma Zamfara baya ga fasinjojin jirgin kasan da ake cigaba da tsare su, 
 
Matsalolin hare-haren yan bindiga na kokarin zama ruwan dare a jihohin Neja da kaduna da Zamfara da katsina da kuma Kebbi inda a kowacce rana ake samun asarar rayuka da kuma sace wasu galibi akan hanyoyi ko kuma a farmakin yan bindiga.