Shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da gwamnonin APC za su yi zama a ranar Talata kan su samar da matsaya a babban taron jam’iyarsu domin cigaban APC.
Shugaban kasa ya dage taron da aka shirya gudanarwa a satin da yagabata tare da gwamnonin kan tafiyar da ta kama shi a kasar Belgium.
Zaman an shirya gudanar da shi ne a tsakanin Shugaban kasa da gwamnonin domin su tattauna a tsakaninsu a fitar da shugaban jam’iyya na kasa da kuma yankunan da za a raba sauran mukaman jam’iyya.
Wata majiya a fadar shugaban kasa ta sanar da cewa za a yi zaman a ranar Talata kwana hudu kafin ranar da aka shata gudanar da babban taro na kasa na APC.
Majiyar da jaridar Nation ta sakaya sunanta ya ce za a yi zaman a Talata kamar yadda aka tsara.
