BUA Ya Gina Asibiti, Makaranta Da Masallaci Na Naira Miliyan 275 A Sakkwato
Join our subscribers list to get the latest news, updates and special offers directly in your inbox
A Laraba data gabata ne kamfanin siminti na BUA ya mikawa al’ummar Gidan Boka da ke Ƙaramar Hukumar Wamakko a jihar Sakkwato wani asibiti da makaranta da masallaci, da kudinsu ya kai Naira miliyan 275.
Kamfanin ya damƙa gine-ginen, wanda tuni aka kammala, har da tagomashin ton 170 na siminti ga al’ummomi 68 a karamar hukumar.
Manajan Daraktan Kamfanin Simintin na BUA, Yusuf Binji, ya ce wannan karamcin wani bangare ne na alhakin yi wa al’ummar da kamfanin ya ke alheri.
Banji, wanda Daraktan Ma’aikata na BUA, Altine Wali ya wakilta, ya ce kamfanin ya gudanar da aikin samar da matsugunan ne a wani bangare na shirin fadada katafaren gini, tare da share filaye a cikin al’ummar Gidan Boka da kuma raba filaye ga iyalan da abin ya shafa.
Da yake jawabi, shugaban gudanarwa da ayyuka na kamfanin, Sada Suleiman, ya ce kamfanin ya kuma gina tituna, da kuma samar da makabarta, ruwan bututu da wutar lantarki ga al’umma.
Ya ce, kamfanin ya tabbatar da shirin raba siminti ga al’umma domin gyara masallatai da sauran ababen more rayuwa, da kuma samar da magunguna da sauran kayayyakin masarufi ga ‘yan kasa a cikin al’ummomin yankin.
“Kamfanin Simintin BUA yana tallafawa al’ummomin a fannin kiwon lafiya, horar da basira, samar da guraben karatu da kayan ilimi,” in ji shi.
managarciya Oct 30, 2021 12 172
managarciya Feb 3, 2025 3 113
Maryamah Dec 14, 2021 2 90
managarciya Jun 24, 2023 5 77
Maryamah Dec 16, 2021 10 75
managarciya Nov 13, 2023 0 550
managarciya Nov 12, 2023 0 346
managarciya Nov 12, 2023 0 335
managarciya Nov 12, 2023 0 416
managarciya Nov 11, 2023 1 702
managarciya Oct 17, 2021 0 789
Kwadayi yana daya daga cikin matsalolin al'umma, kuma ya taka rawa wurin halakar...
managarciya Feb 13, 2025 1 344
managarciya Nov 18, 2021 0 448
Amira Aliyu, ta furta hakan ne lokacin da wasu ke muhawaran, cewa yan matan yanzu...
managarciya Oct 8, 2021 0 423
Wani abu da yafi ciwa da dama daga 'yan Najeriya tuwo a kwarya a Wannan lokaci bai...
managarciya Jul 2, 2023 1 3348
managarciya Jul 15, 2025 0 145
*Su wa suka fi hatsarin kamuwa da cutar?* 1: *Mutanen da ke zaune tare da mai cutar*...