..."Arewa Media Writers" tana kira ga gwamnatin Jihar Kano da su duba yunkurin cutarwa da ake kokarin aikatawa ga al-ummar Anguwar."
Kungiyar marubutan Arewa a kafofin sadarwar zamani "Arewa Media Writers" karkashin jagorancin Shugaban kungiyar na kasa Comr Abba Sani Pantami, da Shugaban kungiyar reshen Jihar Kano Comr Umar Kabir Dakata, tana kira ga gwamnatin Jihar Kano da sauran masu ruwa da tsaki dasu duba yunkurin cutarwa da ake kokarin aikatawa ga al-ummar anguwar Dakata dake cikin kwaryar Jihar Kano.
"Arewa Media Writers" ta samu labari daga Al'ummar wannan yanki cewa; rana tsaka aka wayi gari anzo an gina wannan katafaren waje cikin sirri, duk da kokarin da suke wajen tsaftace anguwar daga munanan dabi'u musamman shaye-shaye da sauran harkokin "Sharholiya" ga matasan yankin.
A binciken da kungiyar "Arewa Media Writers" ta gabatar ta samu labarin cewa mamallakin wajen ya yaudari wadanda ya sayi wajen a hannunsu ne da kuma Dagacin Anguwar Dakata Alhaji Salisu Ibrahim Zubairu, kan cewa gidan Abinci zai bude a wannan waje, haka ne ya bashi dama ya dinga aikin cikin sirri ba'ayi aune ba rana tsaka sai gani akayi an yi Fenti kamar yadda za'a gani a cikin hotuna.
Bayan kammala bincike na tsanaki da Kungiyar "Arewa Media Writers" tayi game da wannan mummanan lamari, a karshe tana mai mika kokenta a madadin Al'ummar anguwan Dakata zuwa ga gwamnatin jihar Kano, da duk masu ruwa da tsaki kan su yi duba zuwa ga wannan aiki, tare da dakatar da barnar nan take, domin ceto tarbiyar Al'ummar wannan yanki.
Muna fatan mai girma Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje zai sharewa al-ummar unguwar Dakata hawaye game da wannan babban iftila'in da ya fado Anguwar don ganin an tseratar da tarbiyar matasan unguwar.