Home Uncategorized Binciken Tambuwal: Ba don a ci zarafin kowa ake yi ba——-Gwamnan Sokoto

Binciken Tambuwal: Ba don a ci zarafin kowa ake yi ba——-Gwamnan Sokoto

9
0

Gwamna Ahmad Aliyu ya karɓi rahoton kwamitin binciken tsohuwar gwamnatin Tambuwal ta PDP

Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmad Aliyu, ya karɓi rahoton kwamitin da ya binciki ayyukan gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal da ya yi zargin ta yi wadaƙa da dukiyar al’umma.

Da yake jawabi, gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta sake naɗa wani kwamiti na musamman domin tabbatar da aiwatar da shawarwarin da kwamitin binciken ya gabatar, da nufin tabbatar da gaskiya, rikon amana da inganta shugabanci a jihar.

Gwamnan ya ce ba don a ci zarafin kowa ake yi ba, kuma ba don murƙushe wata jam’iya ba, abu ne da kundin tsarin mulki ya aminta da shi, ana yi ne don a san yanda aka kashe kuɗin al’umma a cikin shekaru takwas na mulkin gwamnatin da ta gabata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here