Bello Turji Ya Firgita Yana Buya a Ramuka Kamar Beran Daji-----Sojoji 

Bello Turji Ya Firgita Yana Buya a Ramuka Kamar Beran Daji-----Sojoji 


Kakakin rundunar Operation Fansar Yamma, Laftanar Kanal Abubakar Abdullahi ya ce Bello Turji ya dawo kamar beran daji yana buya a ramuka. 
Laftanar Kanal Abdullahi ya ce rundunar ta lalata sansanonin Turji da ke Karamar Hukumar Shinkafi a Jihar Zamfara ta hanyar hadin gwiwar jiragen yaki da sojojin kasa. 
Vanguard ta wallafa cewa an kai farmakin ne bayan Bello Turji ya yi barazanar kai hare-hare kan al’ummar Shinkafi idan har ba a saki danginsa da aka kama ba. 
Laftanar Kanal Abubakar Abdullahi ya bayyana cewa jiragen yakin rundunar Fansar Yamma sun kai farmaki cikin nasara kan sansanonin ‘yan ta’adda da ke Shinkafi. 
“Jiragen yakinmu sun yi mummunan barna ga sansanonin ‘yan ta’adda a Karamar Hukumar Shinkafi. 
An kashe mayaka da dama na Turji, yayin da shi kansa yanzu ke buya kamar beran daji a ramuka.” - Laftanar Kanal Abubakar Abdullahi