Kungiyar jihadi da ta bulla a yankin yammacin Sakkwato tana kara zama barazana ga al'ummar jiha tun bayan da mataimakin Gwamnan jihar ya yi magana kansu hankali ya karkato don sanin abin da suke yi a in da suka yi kaka-gida.
Ƙananan hukumomin Gudu da Tangaza nan ne 'yan bindigar dake raya jihadi suke yi, suke zaune a tare da al'umma musamman a garin Goni da Sarma a gudunmura Ruwa wuri a karamar hukumar Tangaza.
Aminiya ta ji ta bakin wani da yake yankin kan mutanen ya ce mutanen ba su cika takura ba, kuma suna kare mutanen kauyukka daga barayin shanu dake Garkuwa da mutane(bandits), ba su da jituwa da jami'an tsaron Nijeriya, harkokin addini suke yi duk in da suka zo, da baburan tsere suke amfani a cikin yankunan mu.
Haka ma wani ya ce "Dajin Bauri da Sarma da Kaidafi da Kandan su ne in da babbar dabar su take yankin, suna da yawa an ce sun fi su 200, kuma duk wanda ka gani dauke da bindiga biyu zaka gan su, masu garkuwa da mutane suna tsoron su don an fi karfinsu, ana kiransu da Lakurawa masu jihadi.
"A wannan shekara sun takura mutane yankinmu sun hana wasu kauyuka noma, wadanda suka aminta su yi noman yanzu sun ba da kwana 70 kowa ya cire amfanin gonarsa domin za su saki dabbobinsu, a yanzu maganar da nake dake sun rage kwanakin zuwa kwana 10 a wannan Jumu'a ta satin nan wa'adin zai cika, je ka ga yadda mutanen garin Alkasuna da Wariya da Kandam ke cire amfanin gonarsu babu shiri za ka ga wake fari Fes an cire shi domin karamar hasara tafi babba, wasu sun bar Dawarsu a Gona don ba ta kai girbi ba, ya rage nasu su bar ta, ko su sanya dabbobi su canye.
"Mutanen suna da ra'ayin ba a sha da sayar da sigari, duk suka kama shagon da ake sayar da sigari za a karbe tare da yi masa gargadi, ba a sauraren komai a waya sai wa'azi, duk wanda suka kama yana sauraren wakoki ko kallon fim na Hausa za a yi masa hukunci da zai shafi duka ko rasa wayarsa," a cewar mutumin da yake zaune a yankin.
Ya cigaba da cewa mutanen akwai masu jin Hausa a cikinsu amma harshen da suka fi furtawa Fulatanci da Faransanci.
"Mutanen sun tara dabbobi da yawa a yankinmu, sun shigo yanki ba tare da komai ba, sun samu dabbobin ne ta hanyar fitar da Zakkah da suke yi, duk Bafillacen da ke da dabbobi da yawa sukan fitar masa Zakkah su baiwa kansu in ya ki aminta da fitarwa sai su karbe dabbobinsa gaba daya, amma in 'yan bindiga masu Garkuwa suka kwace dabbobin mutum sukan karbo su abaiwa mai abu abinsa, ba su kaiwa gari hari matsalar su da mutane su saba sharadinsu" a cewarsa.
Gwamnatin Sakkwato ta nuna damuwarta kan bayyanar kungiyar ta 'yan ta'adda LUKURAWA.
Mataimakin Gwamna Alhaji Idiris Gobir ya bayyana hakan a Sakkwato ya ce kungiyar mai akidar addini ce a bayanan da suke da shi mutanen nada makamai masu hadari, sun mamaye ƙananan hukumomi biyar na jiha.
A cewarsa wannan abin takaici ne hakan na faruwa a Sakkwato bayan fama da take yi da 'yan bindiga masu satar mutane da dabbobi.
Alhaji Idiris Gobir ya ce suna aiki tare da jami'an tsaron gwamnatin tarayya su tabbatar da kawar da matsalar don kare rayuwa da dukiyoyin al'ummar jiha.
Alhaji Sani Yakubu dan Majalisar tarayya da yake wakiltar ƙananan hukumomin Gudu da Tangaza ya ce yankinsa ya dade yana fama da mutanen su ne ake zargin sun kashe ubankasar Balle a shekarun baya, tsawon lokaci suna zuwa karamar hukumar Gudu ba su dai yi yawa kamar yanzu ba, wani lokaci sukan zo su yi sati ko wata ne su bar wurin tun sanda ana yakar su a kasar Mali sukan zo nan dajin Balle su labe daga baya su tafi.
"Tun bayan daminar nan suke cikin Gudu sun yi sansani a dukkan gefen Gudu kusan ba wani gari da ba karkashin ikonsu ba, sai Balle kadai, a kullum suna fadadawa a yanzu sun shiga kananan hukumomi Binji da Tangaza da Silame, ba su cikin jihar Kebbi don an koro su a can."
Ya yi kira ga gwamnatin Sakkwato ta hada karfi da jami'an tsaro a fitar da mutanen daga yankin kar su yi karfin da za a kasa yakar su.