Home Siyasa Bayar da ilmi daga matakin Furamare har Jami’a kyauta ne a Sakkwato—Abdulmajid...

Bayar da ilmi daga matakin Furamare har Jami’a kyauta ne a Sakkwato—Abdulmajid Sa’adu Haruna Gobir

3
0

Babban maitaimakawa Gwamnan Sakkwato Ahmad Aliyu kan harkokinwayar da kai(SSA Mobilizations) Abdulmajid Sa’adu Haruna Gobir a saqonsa na taya maigirma Gwamna murnar zagayowar ranar haihuwarsa in da ya kai shekara 56 a duniya yi yi kalamai da suka qara fito da nasarar da gwamnan Sakkwato ya samu a shekarru biyu da rabi na mulkinsa.

Abdulmajid ya ce”in aka yi la’akari da irin nasarorin da gwamnatin nan ke samu tun sanda muka shigo a karagar mulki kusan shekaru uku an yi rawar gani a fannoni da dama, in ka duba an yi yekuwar neman zave da kudirori guda 9, a cikin an yi kusan 95 domin yin 100 bisa 100 sai Allah, a harkar ilmi da sufuri da fannin lafiya mai girma gwamna bai yi qasa a guiwa ba, an farfaxo da harkar lafiya tun daga kan matakin farko har zuwa asibitin qwararru ta jiha, ko wannan kasafin wannan shekara ta 2026 an ba da kaso mafi tsoka dan qara inganta sha’anin lafiya a wannan jiha.

“Ilmi na cikin jigo mun ba shi kaso na biyu a wannan shekara don ko da muka zo ilmi na cikin dokar ta vaci a shekara takwas, ashe abin yawuce haka a tafiya da jagorori da suka san abin da suke yi qarqashin jagorancin Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko da mai girma gwamna hakan ya sa aka gyara manyan makarantun gwamnati har guda 17 a cikin qananan hukumomi 23, da samar da kayan rubutu da karatu da aka sayo bayan samar da lilwantaccen wurin karatu, a gefen malamai ana samar musu da gidajen zama a kusa da makarantu.

“A manyan makaratun gaba da sikandare kuma ana biya xalibbai kuxin karatu, a jihar Sakkwato karatu kyauta ne a kowane mataki a qarkshin jagorancin Gwamnan Ahmad Aliyu wannan yana kara nunawa al’ummar Sakkwato ilmi na bunqasa wanda hakan zai haifar da al’umma ta gari wanda hakan zai samar da jagorori nagari.

Kan bukin zagoyawar ranar haihuwar Gwamna Abdulmajid Gobir ya ce “Rayuwar mai girma gwamna aba ce da Allah ya baiwa basira da hazaqa samunsa ba karamin alheri ba ne ga jihar Sakkwato, ka duba rayuwarsa abu ce mai amfani da ta amfanar.

“Tunawa da ranar hihuwarsa shekaru 56 abu ne da zai qara nuna mana Sakkwatawa ba su yi zaven tumun dare ba, sai dai a ce Allah ya qarawa rayuwa albarka.
Haka ma ya yabawa Gwamna kan ware biliyan ɗaya a ciyarwar Ramadan na wannan shekara in da mabuqata za su ci abinci mai inganci a wannan watan don a ranta musu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here