Home Rahoto Bayan kashe mutum xaya ‘yan sanda sun hana Lakurawa tafiya da shanunu...

Bayan kashe mutum xaya ‘yan sanda sun hana Lakurawa tafiya da shanunu da suka sata a Kebbi

8
0

‘Yan sandan jihar Kebbi sun tarwatsa harin da ‘yan bindigar Lakurawa suka kawo a qaramar hukumar Bunza ta jihar Kebbi in da suka kashe mutum xaya a cikin ‘yan bindigar suka hana masu tafiya da shanun gari masu yawa da suka sata.A qoqarin amfani da dubarun zamani ‘yan sanda tare da haxin kan sojoji da sauran jami’an tsaro sun yi hasarar daqile harin satar shanu da ‘yan bindigar da ake kyautata zaton Lakurawa ne a Bunza.A bayanin da jami’in hulxa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Kebbi SP Bashir Usman ya fitar ya ce ‘yan bindigar sai da suka fara kai farmaki a qauyen Tungar Babu Leda in da suka kashe mutum xaya waton Usman Farungu mai shekara 35 kafin zuwan jami’an tsaro anan kuma suka yi yunqurin tafiya da shanu.”‘yan sanda a qarqashin jagorancin babban jami’i a ofishinsu na Kangiwa suka bi ‘yan bindigar da suka tsere har qauyen Garin Mayo a bata kashin da suka yi sun kashe xan bindiga guda suka karvo babura huxu da vatagarin ke amfani da su.”Kange su da aka yi ya tarwatsa aniyarsu ta kai hare-hare da salwantar da rayuwa hakan ya tabbatar da qudirin jami’an tsaro na hana ‘yan ta’adda rawar gaban hantsi, rundunar ‘yan sandan Kebbi tabbatar wa jama’a za ta cigaba da sintiri da aiki da bayanan sirri a jihar, qarqashin tsarin cimma qudirin aikin xan sanda.”Ya yi kira ga mutane su cigaba da ba da goyon baya ga jami’an tsaro da ba da bayanan  gaskiya cikin lokaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here