Bayan Ba Da Miliyan 40 'Yan Bindiga Sun Saki Mutanen Zariya, Sun riƙe  Uku Sai An Kai Musu Babura 3

Mohammed Jalige, Kakakin eundunar, shi ne ya shaidawa manema labarai a Zariya a yau Lahadi, inda ya ce tun a jiya Asabar a ka sake su kuma an ci gaba da ƙoƙarin sakin sauran ma'aikata guda uku. Sai dai kuma Jalige, mai muƙamin ASP,  ya ƙi ya faɗi ko an biya kuɗin fansa kafin sakin ma'aikatan. Amma kuma wata majiya ranta nemi a sakaya sunanta ta shaidawa Kamfanin Daillancin Labarai, NAN cewa ma'aikatan sai da su ka biya naira miliyan 40 sannan a ka sako su. Majiyar ta ƙara da cewa 'yan uwan waɗanda a ka yi garkuwa da su ɗin nen su ka haɗa kuɗaɗen.

Bayan Ba Da Miliyan 40 'Yan Bindiga Sun Saki Mutanen Zariya, Sun riƙe  Uku Sai An Kai Musu Babura 3
Rundunar 'yan sanda ta Jihar Kaduna ta tabbatar da sakin 10 da ga cikin 13 na ma'aikatan ƙaramar hukumar Zariya da ke Kaduna.
Mohammed Jalige, Kakakin eundunar, shi ne ya shaidawa manema labarai a Zariya a yau Lahadi, inda ya ce tun a jiya Asabar a ka sake su kuma an ci gaba da ƙoƙarin sakin sauran ma'aikata guda uku.
Sai dai kuma Jalige, mai muƙamin ASP,  ya ƙi ya faɗi ko an biya kuɗin fansa kafin sakin ma'aikatan.
Amma kuma wata majiya ranta nemi a sakaya sunanta ta shaidawa Kamfanin Daillancin Labarai, NAN cewa ma'aikatan sai da su ka biya naira miliyan 40 sannan a ka sako su.
Majiyar ta ƙara da cewa 'yan uwan waɗanda a ka yi garkuwa da su ɗin nen su ka haɗa kuɗaɗen.
Ta ƙara da cewa kuma masu garkuwa da mutane ɗin ba su saki sauran mutum uku ba saboda sharuɗɗan da su ka gindaya bayan an biya miliyan 40 ɗin nan shi ne cewa za su rike mutum uku har sai an sai musu baburura guda uku sabo fil.
'Yan bindiga suna ci gaba da tunzura jama' a da ba su wahala da raba su da rayukkansu a yankin arewa maso yamma.