BARTER YAM:Sarrafa Doya Na Musamman Domin Iyali
BASAKKWACE'Z KITCHEN
BARTER YAM
ABIN ZAKI BUƘATA
Doya 1/3
Filawa gwangwani 1
Ƙwai 2
Yeast
Mai
Gishiri/ɗanɗano
YADDA ZA A HAƊA
Da farko aunty na za ki dafa doya da dan gishiri da sikari kaɗan
ayi mata yankan suya ko kuma kamar
jinjirin wata.,se ki kwaɓa filawar nan da ɗan yeast amma za
a jika shi da ruwan ɗume ya narke sai a
zuba a cikin kwaɓin
Asa ƙwan aciki bayan an kaɗa shi da ɗan
gigishiri da ɗanɗano a cikin
filawar kada a cika mata ruwa yayi kauri
kauri don ya kama jikin doyar.
.
Idan filawar ta sami ƴan mintina a ajiye a
wuri me ɗumi ko a rana zata tashi sai a
ɗauko doyar a tsoma ta a cikin
dammamiyar filawar sai tsoma a mai bayan
an soya shi a soya doyar har sai jikinta ya
zama kamar ruwan kasa.
MRSBASAKKWACE
managarciya