Home Siyasa Barau ya kori Rashida Mai Sa’a kan zargin yi wa jam’iyyar APC...

Barau ya kori Rashida Mai Sa’a kan zargin yi wa jam’iyyar APC zagon ƙasa

14
0

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya sallami Rashida Adamu, wadda aka fi sani da Rashida Mai Sa’a, daga mukaminta na Mataimakiya ta Musamman a ofishinsa.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Shitu Madaki Kunchi, mai taimaka wa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, ya fitar ranar Litinin, 28 ga Satumba, 2026.

A cewar sanarwar, matakin ya biyo bayan zargin cewa Rashida ta yi kalaman da ka iya tunzura magoya baya, tare da shiga ayyukan da ake zargin suna da nufin raunana jam’iyyar APC, da kuma yin kalaman batanci kan Sanata Barau.

Ofishin Sanata Barau ya kuma ce matakin na zuwa ne bayan wata sanarwa da aka fitar ranar Lahadi, 27 ga Satumba, wadda ta yi zargin cewa wasu mutane na ƙoƙarin lalata muradun siyasar Sanata Barau a Kano da cikin jam’iyyar APC.

Sanarwar ta ƙara da cewa wasu daga cikin mutanen da ake zargi sun taɓa amfana da mukamai da sauran tallafin da Sanata Barau ya bayar, amma daga bisani suka juya masa baya da kuma jam’iyyar.

Ofishin ya bayyana ayyukan da ake zargin mutanen da aikatawa a matsayin yunƙurin raunana Sanata Barau da kuma rage ƙarfin APC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here