Baraden Sakkwato: Malamai sun yi addu'ar samun zaman lafiya a wurin taya shi  murnar  shekara 25 da samun sarautar

Dasuki yana cikin dangin, shi ne ya fara zama Barade kafin a nada shi Sarkin Musulmi a wancan lokacin.

An gudanar da addu'a ta musamman domin samun zaman lafiya a Sakkwato da Nijeriya baki daya a ranar Assabar data gabata.

Addu'ar wadda wadda tsatson Buhari Dan Shehu Usman suka shirya domin taya daya daga cikinsu murnar cikarsa shekara 25 da samun sarautar Baraden Sakkwato waton Alhaji Muhammad Maccido.
Sarkin Malaman Sakkwato Malam Yahaya Na Malam Boyi ya jagoranci addu'ar  a gidan tsohon Sarkin Musulmi Ibrahim Dasuki wanda a Sakkwato ake kira gidan 'Miyati Allah'.

Dasuki yana cikin dangin, shi ne ya fara zama Barade kafin a nada shi Sarkin Musulmi a wancan lokacin.
Bayan yi wa kasa addu'ar zaman lafiya da wucewan wannan lokaci na rashin tsaro da ake fama da shi mai  sarautar ma an yi masa  addu'ar samun lafiya da kwarin guiwa da basirar cigaba da samar da cigaba a cikin al'umma.
Baraden Sakkwato ya nuna farincikinsa ga wannan karimci da 'yan uwansa suka yi masa kuma zai dore da yi wa jama'a hidima kamar yadda ya saba.

Ya ce ya koyi darasi kwaran gaske a shekarun da ya kwashe da wannan sarauta kuma zai cigaba da bayar da shawara mai ma'ana a wuraren da ya dace ga gwamnati da masarautar Sarkin Musulmi.