Bankunan Kasuwanci 20 Sun  Durƙushe  A Nijeriya, Hukuma Ta Sanar Da Masu Hulda Da Su, Su Je Su Karɓi Kuɗinsu

Bankunan Kasuwanci 20 Sun  Durƙushe  A Nijeriya, Hukuma Ta Sanar Da Masu Hulda Da Su, Su Je Su Karɓi Kuɗinsu

 

 Hukumar kula da hakkokin masu ajiya a bankunan kasar nan (NDIC), da ke karkashin Ma'aikatar Kudi, ta kwato kudaden kwastomomi da ke ajiya a wasu bankuna 20 da suka durƙushe. Bello Hassan, shugaban kuma babban direktan hukumar ne ya bayyana hakan yayin da ke jawabi a Abuja wurin taron bajekolin kasa da kasa 

Leadership ta rahoto cewa Hassan ya bayyana kwato kudaden da NDIC ta yi a matsayin cika alkawari da hukumar ta yi na cewa za ta kare kwastomomi idan banki ya durƙushe. 
Shugaban na NDIC, wanda ya samu wakilcin direktan ayyuka a hukumar, Nuhu Bashi, ya yi alkawarin biyan kudaden baki daya ga duk wani kwastoma da ya taho don karban kudinsa. 
"Abin da wannan ke nufi shine, domin jajircewar mu wurin sauya kadarori zuwa kudi, hukumar ta samu isasun kudi da za ta biya dukkan kwastomomi da kudinsu suka maƙalle a bankunan da suka durƙushe." 
Bankunan da abin ya shafa sune ABC Merchant Bank Limited; Allied Bank of Nigeria; Alpha Merchant Bank Pic.; Amicable Bank of Nig. Limited; Commerce Bank; Commercial Trust Bank Limited; Continental Merchant Bank Pic.: Cooperative & Commerce Bank Plc da Eagle Bank; Financial Merchant Bank Limited. 
 
Saura sune Icon Limited (Merchant Bank); Ivory Merchant Bank; Kapital Merchant Bank Limited; Mercantile Bank of Nig. Plc.; Merchant Bank of Africa Limited; Nigeria Merchant Bank Plic.; Pan African Bank Limited; Premier Commercial Bank Limited; Progress Bank of Nigeria; da Rims Merchant Bank Limited.