Bankin Duniya Ya Lissafo Sokoto Da Wasu Jihohi 5 Da Talauci, Rashin Tsaro Za Su Karu a 2024

Bankin Duniya Ya Lissafo Sokoto Da Wasu Jihohi 5 Da Talauci, Rashin Tsaro Za Su Karu a 2024

 

Bankin duniya ya ce rayuwa za ta kara tsanani kuma akwai yiwuwar kashe-kashe su yawaita musamman a wasu jihohin Arewa. 

Punch ta rahoto babban bankin na duniya yana cewa za ayi ta fama da wadannan matsaloli har zuwa watan Mayu na shekarar 2024. 
Jihohin da abin zai shafa sosai sun hada da Borno, Kaduna, Katsina, Sokoto sai kuma Zamfara da wasu bangarori a Adamawa. 
Rahoton da bankin ya fito ya nuna ana fuskantar matsala wajen noma a kasar, hakan zai yi tasiri wajen amfanin gona da za a samu. 
Masana tattalin arziki sun yi hasashen cewa tsadar kayan abinci a 2023 somin-tabi ne kan abin da za a gani a 2024 a jihohin Najeriya. 

Dr. Abubakar Sani Abdullahi ya ce gaskiya abinci zai yi tsada a badi saboda cire tallafin fetur da rashin tsaro sun  jawo an rage noma. 
Kwararren ya ce irinsu wake ba su yi kyau a shekarar bana ba, kuma nan da farkon 2024 za a fara shigowa sayen kayan da aka noma.