Daga M. Shamsudeen, Yobe
Dan takarar majalisar dattawa a mazabar Arewacin Yobe (Zone C), a karkashin jam'iyyar APC, Hon. Bashir Machina, ya karyata jita-jitar da ke cewa ya sayi tikitin din takarar ne domin janyewa Shugaban Majisar dattawan Nijeriya, Sanata Ahmed Lawan, idan ya fadi a zaben fidda-gwani.
Bashir Machina, wanda shi ne tsohon shugaban hukumar kula da sufurin jiragen ruwa ta Nijeriya (Nigerian Shippers Council), ya bayyana hakan a firarsa da manema labaru inda ya ce wannan jita-jita ce maras asali da tushe kuma kirkirarre wanda kuma karya ce tsagwaronta.
Jita-jitar ta ci gaba da nuna cewa, har yanzu Sanata Lawan; dan takarar shugaban kasa, ya na hararar kujerar Sanatan Arwacin Yobe wadda Hon. Machina ya samu nasarar ta a zaben fidda-gwani, kana kuma aboki na kut-da-kut ga Gwamna Mala Buni.
Jita-jitar ta ci gaba da cewa, Hon. Machina, zai hakura ne ya barwa Sanata Lawn idan ya fadi a zaben fidda-gwani a takarar kujerar shugabancin kasa, a karkashin jam'iyyar APC.
Kamar yadda ya gabata, Bashir Machina shi ne ya samu nasara a zaben fidda-gwanin takarar kujerar babu hamayya, wanda tun kafin lokacin zaben wasu daga cikin masu abokanan hamayya suka janye masa, wanda wannan ya na daya daga cikin abubuwan da suka hura wutar wannan jita-jitar domin janyewa Lawan cikin sauki kamar yadda yake a sashe na 35 a dokar zabe (Electoral Act).
Dangane da wannan batu, Hon. Machina ya fayyace cewa, “Na yi imanin cewa Dr. Ahmed Lawan ne kadai zai bayar da wannan amsar, amma domin kore shakka kan jita-jitar, kowa ya sani cewa shugaban majalisar dattawa bai sayi tikitin din tsayawa takarar Sanata ba, face kawai na shugaban kasa ya saya."
“Sannan kuma a tawa fahimta, shi kawai dan takarar kujerar shugaban kasa ne, daga yankin Arewa, saboda haka wannan jita-jita karya ce kuma maras tushe da makama."
Hon. Bashir Machina tsohon dan majalisar wakilai ne, a jamhuriya ta uku, wanda ya sha alwashin yin aiki tukuru domin daukar matakan rage barazanar gurgusowar hamada a yankinsa tare da kirkiro hanyoyin da zasu taimaka domin alkinta saharar ta koma samun hanyoyin kudin shiga, wanda zai sa al'ummar yankin za su ci gajiyarta.
“Kamar yadda ka sani, jihar Yobe na daya daga cikin jihohin da ke fuskantar matsalar hamada a Nijeriya. Sannan a matsayina na dan wannan yankin da ke fama da gurgusowar hamada, zan yi aiki tukuru wajen kawo kudurin dokar da zai kai ga sauya fasalin alkaba'in hamada zuwa hanyoyin samun kudin shiga ga jama'ar mu. Musamman ta la'akari da kasashe irin su Israel, Canada, da Dubai sun riga sun yi nisa kan hakan, kuma muma zamu iya yin hakan." Ta bakin Machina.