Ban Ce Nabar Siyasa Ba Sai Dai-----Bafarawa

Ban Ce Nabar Siyasa Ba Sai Dai-----Bafarawa
Bafarawa


Tsohon gwamnan Sakkwato Alhaji Attahiru Bafarawa ya ƙaryata zancen da ake yi na cewa ya furta yin murabus ga harkokin siyasa.
Bafarawa a hirarsa da RFI ya ce "siyasa kamar ciwon sida ne in ka shiga baka bari don haka ina nan ina siyasa," Bafarawa ya jaddada maganarsa.
Ya ce abin da ya ce ba ya yi shi ne tsayawa zaɓe har ƙarshen rayuwarsa, "mukamin gwamnati kowane iri ne shi ma ban son sa har abada, amma ina da sha'awa a siyasa ta game da wanda zai zama shugaban ƙasa da gwamnan jiha ta,"in ji Garkuwan Sakkwato.
Tsohon Gwamnan na Sakkwato ya ce siyasa ana yi ne don abautawa mutane in na ce na bari ban son bautawa mutane da taimakonsu kenan.
"cewa na bar siyasa ba gaskiya ba ne, a yanzu da nake da shekara 67 ina son na baiwa matasa dama, in na dawo jayayyar muƙami ban kyautawa bayana ba," a cewar Bafarawa.