Bagudu ya kaddamar da sabbin kayan wasa ga kungiyar kwallon kafa ta jihar Kebbi

Bagudu ya kaddamar da sabbin kayan wasa ga kungiyar kwallon kafa ta jihar Kebbi

Bagudu ya kaddamar da sabbin kayan wasa ga kungiyar kwallon kafa ta jihar Kebbi

Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Abubakar Bagudu a ranar litinin data gabata ya kaddamar da sabbin  kayan wasan kwallon kafa da kamfanin auduga na Afrika WACOT ya dauki nauyin samarwa.

Kamfanin shinkafa na WACOT dake  Argungu ne ya kafa kungiyar wasan kwallon kafa ta jihar Kebbi wadda a kwananan ta samu nasara a wata gasar zakaru ta Nijeriya.

style="font-weight: 400;">Kungiyar kwallon mai suna Kebbi Fishers ta zo ta daya a dukkan Afirika a gasar da aka yi wadda hukumar kwallon kafa ta duniya ta shirya ga kungiyoyin kwallo 49 na Afirika.

Kamfanin WACOT ne zai sake daukar nauyin kungiyar ta halarci gasar kasa da kasa da aka shirya a kasar Turai domin wakiltar Afirika gaba daya.

Bagudu ya kaddamar da kayan wasan ne a lokacin da yake karbar kofuna biyu da kungiyar ta lashe, ciki har da wanda ta zama zakara a Nijeriya a gasar da aka yi a jihar Kaduna kwanannan.

Mai baiwa Gwamnan shawara kan harkar yada labarai Yahaya Sarki a bayanin da ya fitar ya ce Bagudu ya nuna farincikinsa ga jagoran kungiyar Mahmud Hadeja kan yadda ya yi jagoranci kungiyar ta zama abar alfahari a Nijeriya da Afrika.

Ya ce ba wani cigaba da kungioyar za ta samu babu goyon bayan masu ruwa da tsaki da ma'aikatar wasanni.

"WACOT tana kokari wajen taimakawa masu basira karkashin jagorancin Faruk Gumel, yana abin da yakamata abin a yaba ne sosai, irin gudunmuwar da muka ba ku za mu yi tsammanin haka a wurinku." a cewarsa ga tawagar 'yan kwallon dake a gabansa.

Bagudu ya roki goyon bayan majalisar dokokin jihar domin karawa kungiyar kudin gudanarwa duba da yadda gwamnatin jihar Kebbi ta dauki nauyin horar da matasa 15 a makarantar bayar da horo kan wasanni dake Ilorin.

"Daya daga cikin matasan da aka horar Zaidu Sanusi Jega yanzu dan wasa ne a kungiyar kwallon kafa ta Nijeriya waton Super Eagle kuma dan wasa ne a FC Porto, dake Portugal." a cewar Bagudu.

Sakataren kungiyar wasan Abdullahi Yahaya ya yabawa Bagudu kan gudunmuwar da yake ba su ya ce shi ne sirrin nasararsu.

"Za mu ci gaba da kokari kan damar da aka ba mu a gida Nijeriya da Afirika da duniya gaba daya."

Ya ce kafin su zama zakara a wasar da aka shura a  Nijeriya sai da suka doke kungiyar kwallon kafa ta Kaduna da Legos da Anambra da Kwara.