Home Rahoto Babban layin wutar lantarki na ƙasa ya sake faɗuwa, karo na biyu...

Babban layin wutar lantarki na ƙasa ya sake faɗuwa, karo na biyu a 2026

9
0

Kamfanin rarraba wutar lantarki na Eko (EKEDC) ya sanar da kwastomominsa cewa an samu faɗuwar tsarin wutar lantarki (system collapse) da misalin ƙarfe 10:48 na safiyar Talata.

Kamfanin ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata.

Sanarwar ta ce: “Masu amfani da wutar lantarki masu daraja, muna sanar da ku cewa an samu faɗuwar tsarin wutar lantarki da misalin ƙarfe 10:48 na safiyar Talata, lamarin da ya haifar da katsewar wuta a dukkanin hanyoyin sadarwarmu.

“Muna aiki tare da abokan hulɗarmu a halin yanzu, tare da fatan a dawo da wuta cikin gaggawa.

“Za mu ci gaba da ba ku bayani da zarar an dawo da wutar lantarki.”

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa an kuma samu irin wannan faɗuwar tsarin wutar lantarki a ranar Juma’a, lamarin da ya janyo katsewar wuta a dukkanin cibiyoyin rarraba wutar lantarki a ƙasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here