BABBAN BURI.
MALLAKAR DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.
SADAUKARWA GA AISHA IDREES ABDULLAHI {SHATU}.
بسم الله الرحمن الرحيم
FITOWA TA SHA HUƊU
~~~Kwanan mu biyu a asibiti sannan muka samu sallama, ƴan kwana kinnan munyi wani irin sabo da Shalelen Hajiya Inna wanda ni kaina bansan lokacin da hakan ta faru ba, sosai yake nuna kulawarsa a kaina da ƴan ƙannena hakan yakan ƙara masa ƙima a idanuwana, itama Hajiya Inna sosai take bamu kulawa, domin kuwa cikin kwanan nan biyu zuwa ta uku asibiti ya yin da gaba ɗaya cinmu itace ta ɗauki ɗawai niyarsa, sai dai har yau Allah be haɗa su su dukan su da mahaifina ba, ko yana fita suna zuwa ko kuwa suna fita yana zuwa haka abin ya kasance.
Jikin Mama ya yi sauƙi sosai bayan mun koma gida munga mutan unguwar da yawa , har waƴanda bamu sa rai ba kuwa.
Da daddare bayan mun kammala gyaran gida muna zaune a tsakar gidan muna fira saiga Baba dasu Umar sun dawo daga masallaci salar isha'i, bayan ya zauna aka kawo masa abinci da na girka mana na taso daga gunda nake nazo na duƙa na ajiye wayar da ya bani a gefen cinyarsa sannan nace "Baba ga wayarnan nan tunda Allah ya bawa Mama lafiya nagode sosai".
Kallona ya yi yana me ajiye cokalin dake hannunsa sannan ya ce "Ayya Khadeejah aini wayar baki ita na yi da sunan ki riƙe gaba ɗaya ba da sunan ki mayar min ba".
Kaina na ƙasa dai bance komai ba yasa hannu ya ɗaukota ya miƙamin a hannuna sannan ya ce "ga tanan kici gaba da amfani da'ita sai dai banda ajiye numbobi barka tai a ciki."
Godiya nayi masa sannan na miƙe na shige ɗakinmu raina wasai dashi, domin kuwa tabbas da ace Baba ya ƙarɓi wayar na tabbata sai nayi masassara kwana biyu.
Da yake dama na sanar da Shalelen Hajiya Inna cewa zan bawa Baba wayarsa karya kira da number sai na samu kaina da zama yanzu na fara typing ɗin mssg ɗin da zan tura masa.
Kwance yake rigin gine yana tunanin irin yadda yake jin zuciyarsa cikin annushuwa kwana biyun nan sai dai lokaci ɗaya komai ke neman kwance masa domin kuwa ajiye wayar Khady tamkar rugujewar farin cikin sane duba da kwana biyu yadda suke ɗan ɗebewa juna kewa ta hanyar waya.
Ƙarar shigowar mssg ne cikin wayarsa ya sanya shi saurin miƙewa ya janyo ta yana me duba mssg ɗin me aka turo masa.
Miƙewa ya yi zumbur sannan ya yi zaune a saman gqdon ya miƙe dukkanin ƙafafuwan sa sama yana me hamdala a gurin Allah sannan ya janyo wayar ya danna calling... Ina ganin kiran naƙi ɗagawa domin kuwa ina tsoron Baba ya jiyo ni daga wajen da yake.
Kiran na tsinkewa na tura masa mssg ina basa haƙurin bazan samu ɗaga wayar ba.
Komawa ya yi ya kwanta sannan ya ce "tabbas nasan ko ban faɗa ba son yarinyar nan nake yi sai dai yaushe hakan ta kasance?".
Ya faɗa a bayyane kana ya ci gaba da cewa "yarinyar ce ta cancanci a sota duba da yadda take da kuma yana yin rayuwarta", "Allah ya mallaka min Khadeejah" ya faɗa yana me sakin murmushin dake ƙara wa fuskansa kyau.
★★★★★★
Yau ta kasance assabar saura sati ɗaya kenan bikin Shalelen Hajiya Inna da Safiya, sosai mutan gidan ke shirye shiryen biki na farko a cikin gidan.
Hankali na idan yayi dubu ya tashi dajin zancen domin kuwa ni kaina nasan zuwa lokacin son Shalelen Hajiya Inna ya riga ya yi man lahani, hakan ya sanya ni yanzu gaba ɗaya ko sashen Hajiya Inna bana ra'ayin shiga domin bana son ganin sa na kanga kamar da gayya ya liƙamin sonsa a cikin zuciyata duk da yasan a kwai wacce yake so kuma yake da buri aure.
Hakan ya sanya ni ko a gida na zama wata shuru shuru duk da magana banci ka yi ba, gaba ɗaya na kashe wayar dake hannuna don bana son jin waƴansu kalamai nasa domin kuwa na tabbata bazan taɓa yadda dasu ba, zanga kamar yaudarata yake yi shi'isa gaba ɗaya naji bana ra'ayin duk wani abu daya dangance sa yanzu.
Sosai hankalin Hajiya Inna ya tashi domin kuwa tunda na fara aiki a gidan ban taɓa share sama da kwana ɗaya ban shiga sashen ta ba, hakane ya tayar mata da hankali , domin kuwa ita ta zaci babban lefi ta yi man.
Zaune yake a gefenta sai faman gwada numberta yake yi amman magar ɗaya ce wayar a kashe take.
Kallon sa Hajiya Inna ta yi kan ta ce "lafiyar ka kuwa?".
"Ina hwa lafiya Hajiya Inna Khadeejah ce gaba ɗaya ta daina ɗaukan waya ta".
Kallonsa ta yi fuskanta cike da alamun tambaya sannan ta ce "wacce khadeejah?".
Sai lokacin yasan daya tafka taɓargaza hakan ya sanya sa kama kame_kame, kallonsa ta sake yi fuskanta cike da alamun zargi sannan ta ce "gayamin wacce Khadeejah?".
Ɗan da kewa ya yi sannan ya ce "Hadeejatu"
"meye a tsakanin ku?," tambayar data jiho masa kenan tana mai tsaresa da idanuwa.
"Bakomai ya faɗa yana me yunƙurin miƙewa.
Hannunsa ta riƙo ta mayar dashi gurin daya tashi sannan ta ce "ko kaine ka sanyata ta daina shigowa sa shennan?", girgiza kai ya yi sannan ya ce "meye ribata idan na aikata hakan?", "To gayamin miye a tsakanin ku ko dai soyayya kuke yi?".
"Kai Allah tsuwarnan kin cika tambaye tambaye haba! Idan ma soyayyar ce meye a ciki?".
"Bakomai Shalele amman naso ka gayamin tsakanin ku domin nasan ta gunda zan fara taron ta".
Duƙar da kansa ƙasa ya yi yana tunanin wai ta gaya mata ko kuwa ya ƙyaleta ne?, ɗan gyara zama ya sake yi a karo na ba'adadi sannan ya langwaɓar da kansa gefe ya yi kalar tausayi sannan cikin ƙasa da murya ya ce "Hajiya Inna sonta na keyi sai dai na rasa ta wacce hanya zan gaya mata, ko zaki taimaka?".
Washe haƙoranta ta yi kai daganin ta zaka tabbar zancen ya faranta ranta sannan tace "kace biyu zaka haɗa lokaci ɗaya Shalele?".
"Dan Allah Hajiya Inna ki daina wannan maganar raina ke ɓaci idan kina yinta , me zanyi da yarinyar da mahaifinta shine sanadiyar war gajewar zuri'ata?, shine ya yanke soyayyar dake tsakanina da mahaifina ta sanadiyar salwantar da rayuwarsa a gaba na."
"Mahaifinta ne mutum na farko dana fara tsana a rayuwata, kuma insha Allahu matuƙar ina raye Hajiya Inna saina durfanar dashi a gaban kotu tayi mana hukunci ni dashi, bazan taɓa yafe masa ba dashi har magoya bayansa masu mayar da alkheree sharri."
Lokaci ɗaya idanuwansa suka juye suka yi jajur dasu, hankalin Hajiya Inna a tashe tace "meye haka Shalele?, gayamin meya ke faruwa?"
Sai da ya yi minti biyu beyi magana ba harta fidda tsammanin zaiyi maganar sai can ya ce "Hajiya Inna yau zan gaya maki abinda baki sani ba, zan sanar dake sirrin dana daɗe ina ajiyewa a cikin zuciya ta, banso na gaya maki ba domin gujewa tado maki da mikin da ya wuce amman yanzu ya zamo dole na gaya maki domin ki tanyeni yaƙi da maƙiyan mu".
Ba tare daya bata hanyar magana ba yaci gaba da cewa "waƴanna da kika gani sune suka kasheman mahaifina a gaban idona, suje suka yiwa mahaifina asirin daya bar gida har yau be waiwayo mu ba, sune sanadin yankewar farin ciki na da har yau be dawo ba, Baba Murtala da Baba Bello sune suka yiwa mahaifina yankan rago a gabana tare da samun goyon bayan Baba Usman Baba Amadu da Baba Sunusi, a lokacin bazan ce maki ga sunan Baba Murtala ba ganin yadda suke da yawa wannan bazai zamo abin mamaki ba."
Tun tana fahimtar abinda yake faɗa harta rasa me yake faɗa ya yinda shi kuwa gaba ɗaya be kula ba, sai jinta da ya yi a jikinsa alamun ta suma kenan.
Dafe kansa ya yi sannan ya ce "abinda nake gudu kenan", sannan ya miƙe a hanzar ce yaje cikin freezer ya ɗauko ruwa masu sanyi ya hau yayyafa mata.
Ajiyar zuciya taja sannan ta fara buɗe idanuwanta ta sauke su a kansa ta ce "..........
Za mu ci gaba a gobe........
ƳAR MUTAN BUBARE CE.