Sabon gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Ahmad Aliyu Sokoto ya kara tabbatar da alkwalin da ya daukarwa mutanen jihar a lokacin yakin neman zabensa na rike jihar Sakkwato cikin adalci da amana.
Ahmad Aliyu bayan ya karbi shedar lashe zaben Gwamna daga hukumar zabe ta kasa reshen jiha a jawabinsa ya ce ba zai ci amanar Sakkwato ba, kuma ba za a hada kai da shi a ci amana ba, "zan tabbatar da samar da tsaro, da yi wa addinin musulunci aiki".
Ahmad Aliyu ya yi kira ga abokan adawa da suka yi takara tare da su zo a hada kai domin ciyar da jihar Sakkwato gaba.
Ya kuma jajantawa mutanen PDP kan faduwa zabe da su rungumi kaddara domin Allah ne bai ba su ba, kuma shi ne ya ba shi nasara.