Ba Zan Yi Kewar Fadar Shugaban Kasa Bayan Kammala Wa'adina---- Shugaba Buhari

Ba Zan Yi Kewar Fadar Shugaban Kasa Bayan Kammala Wa'adina---- Shugaba Buhari

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba zai yi kewar fadar shugaban kasa ba sosai saboda ana yawan kushe shi. 

Buhari ya bayyana cewa yana iya bakin kokarinsa na ganin ya inganta kasar nan amma hakan bai isa ba kuma wasu mutane basa godiya da hakan, jaridar Vanguard ta rahoto. 
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a liyafar cin abinci da iyalai da aminansa suka shirya don murnar cikarsa shekaru 80, a ranar Juma'a 23 ga watan Disamba, rahoton Aminiya. 
Da aka tambaye shi kan abun da zai yi kewa game da shugabancin Najeriya idan ya sauka daga mulki Buhari ya ce "Anya zan yi kewar abubuwa da yawa. Ina ganin ana cin zarafina. 
Na yarda cewa ina iya bakin kokarina amma duk da haka ana raina kokarina. 
"Saboda akwai mutane da suke ganin za su iya razana ni don samun abun da suke so maimakon bin ta tsarin da ya dace don samun duk abun da suke son samu. Kuma akwai wasu mutane da ke son nuna rabin wayo,"
A gefe guda, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya magantu a kan jita-jitan da aka ta yadawa a shekarun baya game da zargin cewa yana yunkurin sake angwancewa da wata. 
Buhari wanda ya yi watsi da lamarin ya ce abu mai kama da haka bai taba faruwa ba kawai dai wasu ne suka kirkiri zance kuma aka yi nasarar yadata a tsakanin al'umma. 
Shugaban kasar ya kuma ce lamarin ya girmama har ta kai wasu yan Najeriya sun yi dafifin zuwa babban masallacin Abuja suna jiran ganinsa domin a daura auren alhalin babu wani batu mai kama da haka daga bangarensa.