Home Siyasa Ba zan maida Kwankwaso safaya taya ba idan na ci zaɓe- Obi

Ba zan maida Kwankwaso safaya taya ba idan na ci zaɓe- Obi

3
0

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya yi alkawarin yin aiki kafada da kafada da mataimakinsa, Sanata Rabiu Kwankwaso, domin magance matsalolin Najeriya idan suka lashe zaben 2027.

Obi ya bayyana hakan ne yayin taron tattaunawa da magoya baya da masu ruwa da tsaki a Enugu, inda ya ce tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma za su kasance cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa za ta ba fifiko.

Ya kuma yi alkawarin ayyana dokar ta-baci a fannin ilimi domin magance matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta da kuma inganta harkokin ilimi a kasar.

Obi ya zargi gwamnatin yanzu da gazawa wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya, yana mai kira ga masu kada kuri’a da kada su yarda da farfaganda da kalaman siyasa marasa tushe.

A nasa bangaren, Kwankwaso ya bukaci ’yan Najeriya da su guji bambancin kabila, su hada kai wajen kawo sauyi, yana mai cewa kasar na fuskantar matsalolin rashin tsaro, talauci, yunwa da rashin aikin yi.

Ya kuma bukaci al’umma su fito kwansu da kwarkwatarsu domin kada kuri’a, tare da kare kuri’unsu har zuwa lokacin sanar da sakamakon zabe.

Shi ma Sanata Victor Umeh ya bayyana tikitin Obi da Kwankwaso a matsayin mafi dacewa da jagorantar Najeriya, inda ya bukaci al’ummar Kudu maso Gabas su hada kai wajen marawa takarar tasu baya a zaben 2027.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here