Ba Za Mu Yi Siyasar Raba Zumunta Ba—Abdullahi Hassan Ga ‘Yan Siysar Sakkwato

Ba Za Mu Yi Siyasar Raba Zumunta Ba—Abdullahi Hassan Ga ‘Yan Siysar Sakkwato

IRIN KALAR SIYASAR DA ZA MU YI KENAN

Tsohon shugaban karamar hukumar Sakkwato ta Arewa jigo a jam’iyar PDP ya bayyana kalar siyasar da za su yi a wannan karon domin ganin sun samu nasarar lashe zaben 2023 dake tafe.

Abdullahi Hassan wasu bayanai da ya wallafa a kan turakarsa ta Facebook ya nuna cewa wannan karon siyasar da za su yi irin wadda suka sa ba ce ta mutunta juna.

Ya ce “ba  za mu yi siyasar raba zumunta ba, tsabtatacciyar siyasa za mu yi, kuma za mu yi nasara da yardar Allah,” a cewarsa.

Wadanan kalaman nasa shagube ne ga sauran ‘yan siyasa dake nufin aiwatar da siyasa ta ko a mutu ko a yi rai ba tare da la’akri da addini da zumunci ba, wanda hakan bai dace ba.

Harkokin siyasa sun soma gadan-gadan duk da manyan jam’iyun siysa a jiha ba su fitar da jadawali da shugabannin da za su jagoranci yakin neman zabensu ba abin da ake gani da cewa siyasar wayo ce suke aiwatarwa don  rage kashe kudi a wannan kakar siyasa  ta 2023.