Ba Wanda Na Yi Magana Da Shi Kan Zan Koma  APC----Sanata Kwankwaso 

Ba Wanda Na Yi Magana Da Shi Kan Zan Koma  APC----Sanata Kwankwaso 
 

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa ba shi da wani shiri a halin da ake ciki  na barin jam’iyyar sa ta PDP zuwa Jam’iyyar APC.

 

Sanata Kwankwaso ya baiyana hakan ne cikin wata hira da ya yi da Gidan Rediyon  DW da ke Ƙasar Jamus kan zancen da ake yadawa zai sauya sheka har an taya masa takarar babbar kujera in ya dawon.

 
 DW ta rawaito Sanata Kwankwaso ya na cewa a yanzu dai ba shi da wata niyyar barin jam’iyyar PDP Zuwa APC,  kamar yadda a ke ta jita-jitar zai bar jam’iyyar saboda rashin gamsuwa  jam’iyyar da yake ciki.
 
“Maganar sauya sheƙa babu ita a yanzu ɗin nan. Ba na magana da wasu mutane kan cewar na  koma APC” inji Kwankwaso.
 
Jita-jita ta yi ƙarfi cewa Kwankwaso zai sauya sheƙa zuwa APC kuma zai sulhunta da abokin burminsa a siyasa, Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje bayan da gwamnan ya kai masa ziyarar ta'aziyyar rasuwar ƙanin sa, Inuwa Kwankwaso.
 
Sai dai kuma a makon nan da mu ke ciki, sai gwamnatin Ganduje ta yi wa Kwankwason raddi kan kalaman da ya yi cewa gwamnan bai ci zaɓe ba a shekarar 2019. 
 
Idan za’a iya tunawa an fara raderadin Kwankwaso da Ganduje za su yi Sulhu ne tun bayan da Gwamna Ganduje ya Kaiwa Sanata Kwankwason Ziyarar ta’aziyyar kaninsa da ya rasu a kwanakin baya.
Kwankwaso ya nuna ba wannan maganar ko a shekarar data gabata an yi ta yada irin wannan jita-jitar kuma lokaci ya wuce ba a yi ba, hakan da ake yi mana wani abu ne da ke nuna darajarsu a siyasa.