Ba Mu Gamsu Da Karin Kwana 10 Ba---Wamakko Ga CBN

Ba Mu Gamsu Da Karin Kwana 10 Ba---Wamakko Ga CBN

Ba Mu Gamsu Da Karin Kwana 10 Ba---Wamakko Ga CBN

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya nuna rashin gamsuwarsa da Karin kwana 10 da babban Bankin kasa ya kara na daina karbar tsoffin kudi a fadin Nijeriya.

Sanata Wamakko a wurin yekuwar neman zaben jam’iyar APC a 2023 cikin karamar hukumar Bodinga ya ce kwana 10 da Gwamnan bankin kasa ya ba da sanarwa kari sun yi kadan don haka za su cigaba da gwagwarmaya har sai talaka ya samu sauki a kasar nan.

Wamakko wanda yake tsohon gwamna ne a Sakkwato ya gamsu sosai ga irin taron jama’ar da ya gani a Bodinga ya ce “da yardar Allah jam’iyar APC ce za ta samu nasara a dukkan zaben da za a yi Sakkwato, don haka a tashi tsaye wajen kare nasarar da za a samu,” a cewarsa.

Ministan harkokin ‘yan sanda a Nijeriya Muhammad Maigari Dingyadi ya ce jam’iyar PDP ta kasa ta ko’ina musamman a jihar Sakkwato da karamar hukumar Bodinga in da bayan wani mataccen aikin ruwa da aka yi ba wani abu da aka yiwa mutanen yankin in kuma akwai shi, na kalubalanci duk wanda  ya san da wani abu ya kawo.

Minista ya yi kira da mutanen jiha su tabbatar da sun kori jam’iyar PDP a mulkin jiha.