Ba Ma Iya Hana Hauhawar Farashin Man Gas A Nijeriya----Gwamnatin Nijeriya

Ba Ma Iya Hana Hauhawar Farashin Man Gas A Nijeriya----Gwamnatin Nijeriya
Ba Ma Iya Hana Hauhawar Farashin Man Gas A Nijeriya----Gwamnatin Nijeriya
 
Karamin Ministan Man Fetur a Nijeriya Timipre Sylver ya ce gwamnatin tarayya ba ta iya kayyade farashin Man Gas a kasar.
Yana karbar tambayoyi ne a gaban manema Labarai dake fadar gwamnatin Nijeriya bayan gabatar da shugabannin albarkatun kasa su Faruk Ahmad ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Ya ce duk Buhari ya damu kan yanda farashin Gas ke hauhawa amma gwamnati ba ta iya sanya tallafi saboda gwamnati ta cefanar da haujin kuma farashin da yake ciki a yanzu shi ne kasuwar Duniya ta aminta da shi.
Ministan ya kara da cewar za su yi kokari su ga farashin ya sauko musamman a lokacin shagalin bukin Kirsimeti dake zuwa nan gaba.