Ba ma buƙatar shirin rance ga malaman jami'o'i - ASUU

Ba ma buƙatar shirin rance ga malaman jami'o'i - ASUU

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ta yi watsi da shirin lamuni da Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar domin ma’aikatan cibiyoyin ilimi na gaba da sakandare, tana mai jaddada cewa abin da gwamnati ya kamata ta yi shi ne ta aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma tsakaninsu tun shekarar 2009.

Shugaban kungiyar na ƙasa , Farfesa Christopher Piwuna ne ya bayyana haka a a yau Alhamis yayin wani taron manema labarai a Jos, babban birnin Jihar Filato.

Jaridar The PUNCH ta rawaito cewa Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin bada bashi ga malaman makarantun gaba da sakandare mai taken 'Tertiary Institutions Staff Support Fund' makonni biyu da suka gabata, wanda aka ƙirƙira domin walwala da tallafawa malamai da ma’aikata da ba ma fannin koyarwa ba  a jami’o’i da sauran manyan makarantu a Najeriya.

Sai dai shugaban na ASUU, yayin taron manema labaran ya bayyana shirin lamunin a matsayin "kashe zuciya" tare da yin kira ga mambobin kungiyar da kada su karbi shirin.

Ya ce: “Mambobinmu ba su da matsala wajen samun lamuni; a zahiri, da yawa daga cikinsu suna cikin bashi mai nauyi daga irin waɗannan shirye-shirye na lamunin. 

"Abin da muke buƙata a yanzu shi ne gwamnati ta sanya hannu kan yarjejeniyar da muka sake tattaunawa da ita, wacce za ta ƙara ƙarfin tattalin arzikin mu na soyayyar kayan masarufi (purchasing power) kuma ta rage dogaro da lamuni daga ƙungiyoyin haɗin gwiwa,".