Home Siyasa Ba ma buƙatar amincewar NDC wajen kafa kwamitin yakin neman zabe –...

Ba ma buƙatar amincewar NDC wajen kafa kwamitin yakin neman zabe – OK Movement

15
0

Ƙungiyar Obi-Kwankwaso (OK) Movement ta ce ba ta bukatar amincewar shugabannin jam’iyyar NDC wajen kafa kwamitin yakin neman zabenta, tana mai cewa kungiya ce mai zaman kanta.

Kungiyar ta bayyana hakan ne bayan da ta kafa kwamitin yakin neman zabe mai mambobi 59, wanda zai gudanar da ayyukan tallafa wa ‘yan takarar jam’iyyar, Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso.

Sai dai Shugaban NDC, Cleopas Moses, ya ce jam’iyyar ba ta amince da kwamitin ba, yana mai cewa shugabancin jam’iyyar ne kadai ke da ikon kafa irin wannan kwamiti.

Da take mayar da martani, Sakatariyar OK Movement, Saadatu Sani, ta ce kungiyar za ta ci gaba da tallafa wa ‘yan takarar NDC, amma ba za ta bar ‘yancinta na gudanar da harkokinta ba.

Ta ce, “Kungiya ce mai zaman kanta, kuma tana da ‘yancin gudanar da harkokinta yadda ta dace.”

Saadatu ta kara da cewa OK Movement tana da tsarin kungiya a fadin Najeriya, tare da kusan mambobi da masu gudanarwa miliyan 2.5, bisa bayanan da kungiyar ta tattara.

Ta kuma bukaci Shugaban NDC, Cleopas Moses, da ya janye kalaman da kungiyar ta bayyana a matsayin bata mata suna, tare da neman afuwa.

Kungiyar ta ce kafa kwamitin na daga cikin matakan da take dauka na karfafa yakin neman zaben Peter Obi da Rabiu Kwankwaso.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here