Ba dole ba ne gwamna ya zama alƙiblar siyasa a kowane lokaci-------Tambuwal

Ba dole ba ne gwamna ya zama alƙiblar siyasa a kowane lokaci-------Tambuwal
Ba dole ba ne gwamna ya zama alƙiblar siyasa a kowane lokaci-------Tambuwal

Ba dole ba ne gwamna ya zama alƙiblar siyasa a kowane lokaci-------Tambuwal

 
Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya nuna al'umma ne ke zama alƙiblar siyasa a jiha da ƙasa akasin jagororin jam'iyya da wasu ke gani.
Gwamna Tambuwal a hirarsa da VOA ya ce ba dole ba ne gwamna ya zama alƙiblar siyasa a kowane lokaci "maganar gwamna ya fita daga PDP ya koma APC su 'yan jiharsa sun san abin da suke ji, al'ummar da yake wa jagoranci sun san abin da suke ciki in lokaci ya yi na su yi wa kansu alƙalanci da hukunci za su kalli halin da suke ciki yanzu su yi wa kansu alƙalanci." a cewar Tambuwal.

Ya cigaba da cewa 'yan ƙasa ake magana don su ke ji a jikinsu a halin da ake yanzu ƙarƙashin gwamnatin APC, mun faɗa tun farko in gwamnatin nan ta ɗore halin da ake ciki yanzu zai cigaba na rashin tsaro da faɗuwar darajjar nera, 'a tsarinmu mun yi hasashe abin da ke zuwa yana dawowa bisa ga sanin da Allah ya ba mu' in ji shi.
A jawabin na Tambuwal wanda Managarciya ta samu ya nuna rashin jindaɗinsa ga sauya sheƙar Femi Fani Kayode "PDP ta yi rashin FFK ba za ka ji daɗi ɗan jam'iyarka ya fita ya koma wata ba, amma kuma jama'a su ne alƙalai kan wane ne FFK al'umma ne za su yi magana kansa da muhimmancinsa a siyasa", Tambuwal ya yi shaguɓe.

Da ya juya kan raɗe-raɗin sauya sheƙar Jonathan ya ce yana kira da Jonathan ya riƙe abin da yake da shi na mutunci, a gefen Shugaba Buhari kuma ya duba abin da ya faɗa kan Jonathan, ko wannan Jonathan daban ne da wancan na 2015 ko Buhari ya kasa ne Jonathan yafi shi iyawa.