Watan Azumin Ramadan na shekarar 2026 ya zo da wani siga da saban ba a jihar Sakkwato.
Kafin soma a ibadar ta Azumin da yawan mutane sun za ci za a fara shi cikin tsananin zafin rana a yankin na Sakkwato, amma sai aka samu akasin haka in da sanyi ya dawo abin da ya jefa masu sana’ar qanqara cikin hasara domin da yawansu sun yi tanadin samun kuxi a sana’ar.
Wasu daga cikinsu sun sayi sabbin Firjin masu qanqara a qaramin lokaci, tare da haxa wutar Sola ganin wutar Lantarki ba ta da tabbas a wannan qasar ta Nijeriya.
Harkar Qwai da ba ta katsewa saboda azumin Ramadan anan ne aka samu sabon lamari in da qwan kaji ya fara yankewa tun a daren ranar da aka ba da sanrwar ganin wata kiret farashinsa ya tashi daga 5800 zuwa 6500, ana wayewar gari xaya ga Ramadan a birnin Sakkwato qwai ya yanke bubu shi wurin masu sayarwa, abin da ba a tava gani ba a jihar.
Hamisu Muhammad da yake sana’ar qwai kasuwar kayan miya ta Abu Kure ya ce yafi shekara 40 yana sana’ar sayarda qwai amma bai tava zama babu shi ba, sai a wannan shekara abin ya ba shi mamaki sosai.
“Na xaura yankewar qwan kan mutane ne suka qara yawa masu son yin amfani da shi, manyan ‘yan kasuwarmu da ke xauko qwan a Kudancin Nijeriya ba su sawo ba a tunaninsu yawan qwan da ake da shi a qasa zai isa, sai abin ya canja an saye wanda ake da shi a jiha kuma ba a sawo daga waje ba.
“Ka ga tun da lamari ne na buqatar gaggawa duk wanda ya samo dole zai qara farashi a yanzu duk in da ka ganshi ana sayar da qwara xaya kan 320 wani wuri 350 kiret kan 9000 wani wuri 9500,” a cewarsa.
Usman Shehu ya ce yankewar qwai da aka samu yana ganin matsala ce ta barin kiyo da yawan mutane suka yi a jihar domin tun a baya masu noman qwai a jihar ba su iya wadatar da jiha da qwan sai an shiga da shi daga maqwabta.
“Matsalar tavarbarewar tattalin arziki da muke da shi a qasar nan ya taimaka sosai ga wannan lamari domin da yawan masu kiyon kaji a jiha sun daina, domin tsadar abincin Kaji, gare su ne ake samun sauqi mutum ya je gona ya sawo abinsa ya kasa yana sayarwa.
“Ni ina sawo qwai daga Ogun na kawo Sakkwato amma na bari domin tsadar kuxin motar kawo shi za ka ga in ya zo ka cire wanda ya fashe in ba ka yi sa’a ba kai da ke neman riba sai ka ga faxuwa, da yawanmu muka dawo muna saye ga mutanenmu a jiha ko a Zamfara ko a Kebbi, wasu masu harkar kiyon sun dakatar kan abincin Kaji ya yi tsada, mai sayarwa ba ya da riba kaga dole a bari yanzu kiret ya kai dubu 10 ake sayar da shi, xaya-xaya kan 420,” in ji shi.
Wani magidanci Yusuf Labbo ya ce cin qwai ai ba dole ba ne ni’ima ce in kana da ka saya don haka ni sanda na je sayensa a farko azumi babu haka na haqura da na koma a ukun azumi na same shi kan 320 haka na daure na sayi uku domin a sanya ga doya mu ci ni da yara da mata.
Ya ce na huquara da cinsa sai ya koma farashin na baya ya dawo a 200 da muke sayensa tun da ‘yan kasuwar sun cire tausayi sai sun matsar da mutane.
Karima Bawa ta ce gaskiya bai kamata qwai ya yi wannan tsadar ba ina laifin ya qara farashi ko da kaxan ne kamar yadda man girki ya yi kafin Azumi ana sayar da shi kan 1800 kwalba yanzu ya koma 2000, amma a ce shi qwai ya gagari talaka, duk waxanda suka san su ne masu matsala su ji tsoron Allah su gyara a wannan lokacin na Ramadana.
“Qwai fa ya gagari talaka duk in da ka ganshi ana ci gidan masu hali ne ko ya yi sa’a mai hali ya ba su kyauta, ina talaka zai iya ba da 400 a ba shi qwai guda tal haba tun da ba shinkafa ba ce ai sai a haqura,” in ji Karima.





