Home Rahoto Azumi 30 za a yi a Nijeriya a cewar Sarkin Musulmi

Azumi 30 za a yi a Nijeriya a cewar Sarkin Musulmi

2
0

Ba a ga watan Shawwal a Nijeriya ba—-Sarkin Musulmi

Majalisar Sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar tare da hadin guiwar kwamitin ganin wata na kasa ba su karbi rahoton ganin watan Shawwal ba a ko’ina.

Rashin ganin watan ya sa majalisar ta aiyana Jumu’a ta zama 1 ga watan Shawwal na shekarar 1447 daidai da 20 ga Maris na 2026.

Alhamis za ta zama 30 ga watan Ramadan ganin watan bai bayyana ba a Nijeriya.

Sarkin musulmi ya yi wa al’ummar kasa barka da shan ruwa haka ma ya roki jama’a su cigaba da ibada da ayukkan alheri.

“A cigaba da yin addu’oin samun zaman lafiya da aminci da kwanciyar hankali da samun sauki na jarabawar da ake ciki.

“A yiwa jagorori addu’ar Allah ya daura su kan abin da zai zama maslaha da alheri ga wannan kasa,” a cewar sarkin musulmi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here