Atiku ya zargi Tinubu da hannu a rikicin ADC har ya na baiwa Nafiu Bala tsaro
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi zargin cewa shugaban tsagin jam’iyyar ADC, Nafiu Bala, na tafiya da manyan motocin tsaro kamar gwamnan jiha.
Atiku ya yi zargin cewa wannan sabon sauyi a rayuwar Bala na samun tallafi ne daga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da DW Hausa, inda ya kuma danganta rikicin da ke addabar jam’iyyar ADC da tsoma bakin wasu masu ruwa da tsaki k.
A cewarsa, jam’iyya mai mulki na nuna damuwa da yadda ADC ke ƙara samun karɓuwa a faɗin ƙasar nan.
“Har yanzu mutane daga dukkan jihohi na ci gaba da shiga jam’iyyar. Babu wata alama da ke nuna cewa ‘yan Najeriya na janyewa daga goyon baya,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa abin da ke faruwa tsoma baki ne daga wajen jam’iyya, inda ya zargi wasu mutane da karɓar kuɗi domin su yi aiki da wasu muradu da ke ganin cigaban jam’iyyar a matsayin barazana.
Atiku ya kuma yi tambaya kan yadda Bala ya samu tsaro da kayan more rayuwa, yana mai cewa hakan na nuna akwai wani tasiri daga waje.
“Ta yaya wanda ya ce shi ne shugaban jam’iyya zai samu tsaro, motoci da mazauni cikin gaggawa? Wannan na nuna akwai wani tasiri daga waje. Muna da hujjoji, mun san inda yake zaune da yadda yake motsi kamar gwamna,” in ji shi.





