Atiku Ya Yarda Kuskurensa Kan Abin Da Suka Yiwa Tsagin Wike

Atiku Ya Yarda Kuskurensa Kan Abin Da Suka Yiwa Tsagin Wike
 
Ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarkashin inuwar jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, yace bai hakura ba har yanzu yana tattauna wa da mambobin da suka fusata domin shawo kan rikicin da ya addabi jam'iyyar.
Daily Trust ta tattaro cewa Atiku ya yi wannan furucin ne ne a jihar Gombe, jim kaɗan bayan buɗe sabon Ofishin da jigon PDP, Jamilu Isiyaku Gwamna, ya ba shi.
Tsohon mataimakin shugaban kasan ya nuna alamun kwarin guiwa da cewa rikicin da ya ƙi ci kuma ya ki cinye wa za'a warware shi kuma PDP zata tunkari zaɓen 2023 da ƙarfinta. 
Alhaji Atiku ya ƙara da cewa har yanzun PDP shahararriyar jam'iyya ce kuma mafi daɗe wa a Najeriya, haka nan ita ke da damar lashe zaɓen shugaban ƙasa da ke tafe a 2023.