Kisan gilla: A ziyarar da Tinubu ya kai jihar Plateau ko sauka daga jirgi bai yi ba ya gama da ƴan garin da abin ya shafa— Atiku.
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya soki Shugaba Bola Tinubu kan ziyarar da ya kai Jihar Plateau, inda ya zarge shi da gaza kai ziyara kai tsaye ga wadanda rikicin ya shafa, yana mai cewa shugaban ya tsaya ne kawai a filin jirgin sama ya gana da al’umma.
Atiku, a cikin wata sanarwa da Babban Mataimakinsa na Musamman kan Harkokin Sadarwa da Yada Labarai, Phrank Shaibu, ya fitar, ya bayyana ziyarar a matsayin “alama mai tayar da hankali ta nesanta kai” daga halin da ‘yan Najeriya ke ciki sakamakon matsalar tsaro.
A cewar tsohon mataimakin shugaban kasar, shugaban bai ziyarci al’umma da abin ya shafe suba, haka kuma bai gana da iyalan da ke cikin jimami ko kuma wadanda suka jikkata da ake kula da su a asibitoci ba.
Ya kara da cewa, da alama an takaita ziyarar cikin gaggawa ne domin shugaban ya wuce Lagos domin hutun Easter, matakin da ya ce ya nuna rashin dacewa a gaban wata babbar masifar kasa.
Har ila yau, ya soki abin da ya kira mayar da ziyarar wani taron siyasa, yana mai ikirarin cewa shugaban ya gana da magoya bayan jam’iyya a Jos maimakon yin hulda kai tsaye da wadanda abin ya shafa.
Atiku ya danganta lamarin da wata ziyara da shugaban ya kai Jihar Benue a watan Yunin shekarar 2025, inda ya ce an ga irin wannan salo lokacin da shugaban bai kai ziyara zuwa cibiyar hare-haren da suka faru a Yelwata ba.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma yi zargin cewa ba a sanar da wata takamaimiyar manufar gwamnati ko wani tsayayyen matakin tsaro ba a yayin ziyarar ta Filato, lamarin da ya kara jefa shakku kan yadda gwamnati ke tunkarar karuwar matsalar tsaro.
Haka kuma, ya soki rahotannin da ke cewa an dauko wasu mazauna wurare daban-daban na Jos aka kai su filin jirgin sama domin tarbar shugaban, yana mai bayyana hakan a matsayin wani yunkuri na tsara ziyarar domin nuna abin da ba’a zahiri ba.
Atiku ya yi tambaya kan yadda gwamnatin ke da kudurin magance matsalar tsaro, yana mai cewa ‘yan Najeriya na bukatar fiye da ziyarce-ziyarce na nuna alama kawai.
Ya jaddada cewa, har sai gwamnatin ta daina abin da ya kira “nuna hoton siyasa” ta koma kan daukar matakai masu karfi da suka shafi rayuwar jama’a kai tsaye, irin wadannan ziyarce-ziyarce za su ci gaba da kasancewa ba su da alaka da hakikanin halin da al’umma ke ciki.






