Atiku Ya Sayi Fom Na Takarar Shugaban Kasa, Tambuwal Yana Kan Shawara

Atiku Ya Sayi Fom Na Takarar Shugaban Kasa, Tambuwal Yana Kan Shawara

 

Rashin tabbas kan yankin da zai samar da shugaban kasa a jam'iyar PDP har yanzu ba a magance shi ba abin da ya kai ga kafa kwamitin mutum 37 domin su aiwatar da aikin tare da amincewa za a sha duk abin da suka dama kan yanda jam'iyar za ta tsayar da dan takarar shugaban kasa.

Jagorori biyu daga Arewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal sun yi nisa kan takarar ta su, ta neman tsayawa shugaban kasa a inuwar PDP.
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar wata kungiyar 'yan kasuwa daga yankin arewa maso gabas sun saya masa Fom na takarar wanda ake sayarwa kan miliyan 40, awa 24 bayan jam'iyar ta aminta ta fara sayar da fom ga masu takarar kowace kujera a cikin jam'iyarsu.
Wata majiyar ta tabbatar da cewa Atiku zai aiyana tsayawarsa takarar shugaban kasa a jam'iyar PDP a ranar Talata mai zuwa.

Haka kuma Tambuwal ya ce yana kan tuntuba ne kan takararsa ta shugaban kasa.